Starlink yana aiki a wasu ƙasashen Afirka irin su Nijeriya:Hoto/Reuters

Chadi ta ce ta ba da lasisi ga kamfanin samar da intanet na Starlink na attajirin duniya Elon Musk domin inganta intanet a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.

Starlink wanda wani ɓangare ne na kamfanin SpaceX yana aiki wasu ƙasashen Afirka amma ya fuskanci ƙalubalen tsare-tsare da tsaiko daga kamfanonin sadarwa mallakar gwamnati daga wasu ƙasashen yankin.

"Mun fara tattaunawa da kamfanin Starlink tun shekarar 2021 kuma mun cim ma yarjejeniya kan muhimman batutuwa," in ji Ministan Sadarwar Chadi Boukar Michel a hirarsa da kamfanin dillancin labaran Reuters ta waya.

Ƙididdigar Bankin Duniya ta baya bayan nan na nuna cewa kashi 12 cikin 100 na mutanen Chadi ne ke samun intanet a shekarar 2022.

"Mafi yawan wurare a ƙasarmu ba su da layin intanet (fibre optics) kuma na yi imanin cewa Starlink zai taimaka mana cike wannan giɓin," a cewar Michel, yana mai ƙarawa da cewa ingantaccen intanet zai taimaka su mayar da ayyukan gwamnati ta intanet a wurare masu nisa tare da kafa sabbin kamfanoni masu alaƙa da fasahar intanet.

"A yanzu Starlink ya samu a Chadi!" kamar yadda Musk ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin. Kamfanin mai samar da intanet yana aiki a wasu ƙasashen Afirka ciki har da Zimbabwe da Nijeriya da Mozambique da Malawi da Madagascar da Benin da Sudan ta Kudu da Eswatini da kuma Saliyo.

A farkon shekarar nan ne dai mahukunta a Kamaru suka ba da umarnin ƙwace na’urorin Starlink a tashoshin jiragen ruwa domin ƙasar ba ta bai wa kamfanin lasisin aiki ba.

Shi kuwa kamfanin sadarwa mafi girma a Kenya Safaricom ya yi kira ga mahukunta su yi nazari kan yiwuwar umartar kamfanonin samar da intanet masu amfani da tauraron ɗan'adam irin su Starlink su yi aiki tare da kamfanonin sadarwa na cikin gida a ƙasar.

TRT Afrika