Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Ghana ya ce ya samu nasarar karbo Cedi biliyan 3.1 cikin biliyan 5.7 da yake bin kwastamominsa bashi.
Kamfanin na ECG ya ce ya karbi wadannan makudan kudaden ne cikin wata guda.
A kwanakin baya ne kamfanin ya kaddamar da wani shiri na musamman na karbo basussukan da yake bin kamfanoni da gidaje da shaguna da sauran wuraren da ke amfani da lantarki.
A yayin wani taron manema labarai, Daraktan ECG Mista Samuel Mahama ya bayyana cewa kamfanin na shirin fitar da wani tsari na karbo wasu kudade da suka kai Cedi biliyan daya, wadanda suna cikin jumullar bashin da kamfanin ke bi na biliyan 5.7.
Ya bayyana cewa daya daga cikin kalubalen da suke fuskanta shi ne sun kasa gano wasu kwastamomi da suke bi bashin Cedi miliyan 780.
A cewar Mista Mahama, cikin kwastamomin akwai kamfanoni 200 da suka daina aiki sakamakon karayar arziki ko kuma durkushewa.
Ya kuma karawa da cewa kamfanin ya kasa gano wasu kwastamomin nasa da ake bi Cedi miliyan 750 wadanda ba su amfani da mitar kati sakamkon ko dai an rusa wuraren nasu ko kuma wani bala’i ya afka musu.
Game da amfani da lantarki ba bisa ka’ida ba, daraktan ya ce sun gano wurare 300,000 da suke shan wuta ta haramtacciyar hanya.
A kwanakin baya ne dai wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya ce a kasar Ghana aka fi samun wutar lantarki a yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.
Rahoton ya ce kimanin kashi 80 cikin 100 na mutanen Ghana ne ke samun wutar lantarki.