Gwamnatin Kamaru ta tura sakatarenta Ferdinand Ngoh Ngoh, a matsayin jakada na musamman zuwa kasar Chadi, ‘yan kwanaki bayan da gwamnatin Chadi ta yi wa jakadanta a Kamaru kiranye.
Gidan talabijin na ƙasar Kamaru ya ce sakataren gwamnatin Kamarun ya gana da Shugaban Chadi, Mahammat Idriss Deby, kuma ya mika masa sako daga shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya.
Duk da cewa sanarwar da gidan talabijin na gwamnatin kasar Kamaru ya wallafa a shafinsa na Twitter bai yi karin bayani kan aiken ba, ga alama ba zai rasa nasaba da sulhu kan sabanin da ya kunno kai tsakanin kasashen biyu ba a baya-bayan nan.
A makon da ya gabata ne gwamnatin Chadi ta yi wa jakadanta a Kamaru kiranye bayan rahotanni sun fito cewa kamfanin man Kamaru ya sayi kashi 10 na hannayen jari daga kamfanin makamashi mai zaman kansa na kasar Birtaniya na Sahara Energy.
Kafin wancan lokacin, kamfanin Sahara Energy ya sayi hannayen jarin kadarorin mai daga kamfanin Exxon Mobil da ke kula da bututan man fetur na Kamaru da Chadi.
Chadi ta ce ba ta yarda da cinikin da aka yi tsakanin Sahara Energy da Exxon Mobil ba.
Saboda haka sai ta karɓe iko da duk kadarorin man Exxon Mobil a kasarta don yarjejeniyar da kamfanin ya kulla da Sahara Energy ya saba wa yarjejeniyar da ke tsakanin gwamnatin Chadi da Exxon Mobil.