Tsohon Sarkin Kani Muhammadu Sanusi II ya ce akwai bukatar duka 'yan Nijeriya da Nijar su bayar da gudunmawarsu wurin shawo kan wannan matsalar, Hoto/Others

Daga Abdulwasiu Hassan

Juyin mulkin da aka yi a Nijar na neman zama wani abu da ke son kure hakuri da juriya ta turbar dimokuradiya, inda lamarin ke kokarin tilasta wa kungiyoyin yankuna kamar su Kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS da Kungiyar Tarayyar Turai amfani da karfin soja.

Jagororin juyin mulkin sun kafe kan ci gaba da zama a mulki duk da matsin lamba da barazanar soji da suke fuskanta.

A halin yanzu an mika lamarin ga sarakuna da Malaman addini domin tabbatar da sulhu ganin cewa duka hanyoyin diflomasiyya da aka saba amfani da su sun ki bullewa.

Malaman addini da sarakunan na gargajiya na haduwa da takwarorinsu na Nijar domin shiga tsakani.

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya je Yamai ranar 9 ga watan Agusta inda ya gana da jagoran juyin mulkin Nijar, Abdourahmane Tchiani, kwana guda bayan sojojin sun ki yarda su karbi bakuncin wakilan kungiyoyin Tarayyar Afirka da MDD da ECOWAS.

Kafin nan, ECOWAS ta tura Shugaba Patrice Talon na Jamhuriyyar Benin, da tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmin kasar Muhammad Sa’ad Abubakar, domin tattaunawa da sojojin Nijar.

Gwamnatin mulkin sojan ta ki amincewa da dukkansu.

A daidai lokacin da Muhammadu Sanusi na II, wanda shi ne Khalifan Tijjaniya a Nijeriya, ke tattaunawa da shugaban sojin na Nijar, shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu kuwa na bai wa wata tawagar malaman addinin Musulunci na kasar damar shiga tsakani kan matsalar ta Nijar.

Shugabannin addini na Nijeriya sun ce bukatarsu ta zuwa Nijar "ta biya". Hoto/ActuNijar

“Ana ci gaba da shiga tsakani, kuma za mu ci gaba da yin iya kokarinmu domin hada kan bangarorin biyu su fahimci juna. Wannan lokaci ne na diflomasiyya. Ba batu ba ne da za mu bar wa gwamnati,” kamar yadda tsohon Sarkin ya shaida wa manema labarai a Abuja bayan da ya mika sakon sojin na Nijar ga shugaban Nijeriya.

Nasarorin farko

“Akwai bukatar duka ‘yan Nijeriya da ‘yan Nijar su hada hannu wajen nemo hanyar da za ta taimaka wa Afirka da mafita ga Nijar, da kuma wadda za ta taimaki bil adama,” in ji shi.

A ranar Asabar, sojojin Nijar sun bayyana cewa a shirye suke su tattauna da kungiyar ECOWAS.

Wannan ne karo na farko da jagororin juyin mulkin suke nuna alamun bude kofa domin tattaunawa da kungiyar.

Wannan na zuwa ne bayan wata ziyara da Malaman Addinin Musulunci masu fada a ji daga Nijeriya suka kai Yamai inda suka hadu da shugaban sojojin na Nijar Abdourahamane Tchiani a Yamai.

Firaiministan Nijar, wanda sojojin kasar suka nada, Ali Mahamane Lamine Zeine, ya shaida wa manema labarai cewa Janar Tchiani ya nuna alamar tattaunawa da ECOWAS.

Da aka tambaye shi ko sojojin sun shirya tattaunawa da ECOWAS, sai Firaiministan ya ce: "Eh, tabbas. Wannan shi ne abin da shugabanmu ya shaida musu, bai ce ba zai tattauna ba.

“Mun amince kuma shugaban kasarmu ya nuna alamun tattaunawa. A yanzu za su tafi su shaida wa shugaban Nijeriya abin da suka ji daga gare mu... muna sa ran a kwanaki masu zuwa, su (ECOWAS), za su zo nan su same mu domin tattaunawa kan yadda za a cire takunkuman da aka saka mana,” in ji shi.

Shugabannin juyin mulki a Nijar sun ce a shirye suke su tattauna da ECOWAS. Hoto/Others

Firaiministan ya bayyana takunkumin na ECOWAS, wanda ya soma jefa 'yan kasar cikin wahala a matsayin “rashin adalci” kuma ya saba wa ka’idojin kungiyar.

Sai dai ya ce dage takunkumin ba wani sharadi ba ne na tattaunawa. Shugaban ayarin malaman da suka tafi Nijar, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa maneman labarai cewa suna Nijar domin “yin sulhu.”

Ya ce sun shaida wa shugaban sojin cewa tattaunawa na da muhimmanci domin magance wannan rikicin. Sheikh Bala Lau ya ce kafin tafiyarsu Nijar, sun shaida wa Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne shugaban ECOWAS, cewa bai dace a yi amfani da karfin soji domin shawo kan matsalar ba.

Sheikh Bala Lau ya ce burinsu na zuwa Yamai “ya cika” ta bangaren kokarin shawo kan sojojin kasar domin a tattauna.

Ya kuma ce ba su hadu da Shugaba Bazoum ba domin hakan ba ya cikin tsarinsu.

Duk da cewa a kundin tsarin mulki ba su da wata rawa da za su iya takawa kan lamarin ba, amma sarakunan gargajiya da malaman addini na da karfi wurin juya ra’ayin jama'a.

‘Yan uwantaka ta tarihi

Nijar, kamar sauran arewacin Nijeriya, kasa ce wadda akasarinta Musulmai ne kuma Hausa na daga cikin manyan harsunan kasar.

Akasarin mutane daga arewacin Nijeriya da Nijar na da addini da al'ada da harshe daya. Hoto/Reuters

Wasu daga cikin sassan Nijar da Nijeriya a hade suke a zamanin Turawan mulkin- mallaka a jihohi kamar su Sokoto da kuma wasu da suka fita daga kasar.

Sojojin Birtaniya da suke mulkin-mallaka sun kwace iko da kusan duka yankunan da ke karkashin Sokoto, inda Faransa kuma ta dauki sauran.

Bayan samun ‘yancin kai, duka kasashen sai suka rinka amfani da harsunan iyayen gidansu, inda Nijar ta dauki Faransanci sai Nijeriya kuma Ingilishi. Duk da bambancin harshe, ba a samu matsaloli na addini ko zamantakewa tsakanin bangarorin biyu ba.

Tasirin Addini da Gargajiya

Duka wadannan sun yi bayani kan dalilin da ya sa malaman addini suke da tasiri ta bangaren kokarin shawo kan rikicin Nijar.

Farfesa Kamilu Sani Fagge na Tsangayar Nazarin Siyasa ta Jami’ar Bayero da ke Kano na ganin juyin mulkin Nijar zai iya zama wani sanadi na nuna muhimmancin sarakunan gargajiya.

“Idan ka kalli Nijeriya da Nijar, mutane ne iri daya. Suna tare kafin mulkin-mallaka. Don haka ana ganin darajar sarakunan gargajiya da malaman addini. Za mu ga irin tasirin da za su yi fiye da tsarin gwamnati,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Amma Dakta Aminu Hayatu na Jami’ar ta Bayero na ganin dalilin da ya sa yake ganin sojojin suna sauraren jagororin addini saboda su ba su yi musu barazana ta afka musu da karfin soji kamar yadda ECOWAS take yi.

ECOWAS ta yi barazanar amfani da karfi a matsayin makamar karshe domin dakile juyin mulkin Nijar. Hoto/others

“Sarakunan gargajiya na da muhimmanci sosai wuri tattaunawar diflomasiyya ganin cewa ba sa cikin gwamnati,” in ji shi.

“Ba wai sojojin sun fi sauraren sarakunan gargajiya ba ne fiye da jagororin mulkin dimokuradiyya ko ECOWAS, amma hanyar da sarakunan gargajiyar ke bi ta fi ta amfani da karfi. Sojojin na kallonsu a matsayin abokan kawo ci-gaba da kuma masu tattaunawar zaman lafiya wadanda za a iya saurare a zahiri.”

Iyaka

Tun da duka sarakunan gargajiya da kuma malaman addini sun soma kokarin shawo kan wannan matsala, tambayar da ke bakunan masu sa ido ita ce: Har wane mataki za su kai wurin shawo kan matsalar?

Duk da cewa wasu suna ganin za su iya magance matsalar, amma wasu na ganin ba lallai ba. Farfesa Fagge na ganin sakamakon irin tasirin sarakunan gargajiya da malaman addini a kasashen biyu, za su iya taimakawa wurin magance rikicin, musamman idan aka ba su cikakken goyon baya.

“Ina tunanin wannan zai taimaka wurin kwantar da hankali...Dalilin da ya sa ba a karbi tawagar Abdulsalami da Sultan ba shi ne saboda ECOWAS na yi musu barazana. Idan ba haka ba ana ganin girman Sarkin Musulmi a Nijeriya da Nijar,” in ji shi.

An hana tawagar da ECOWAS ta tura Nijar karkashin jagorancin tsohon shugaban Nijeriya Abdulsalami Abubakar ganawa da shugaban sojin Nijar Tchiani. Hoto/Others

Duk da haka, Dakta Hayatu ya yi gargadi cewa ta hanyar sarakunan gargajiya da malaman addini ba za a iya samun mafita nan take ba, kamar yadda mutane da dama suke zato.

“Akwai bukatar ku fahimci cewa ba wai batu ne kadai na tattaunawa ba, akwai yiwuwar sarakunan gargajiyan za su soma tattaunawa da jagororin sojoji amma hakan ba ya nufin sojojin za su mika mulki. Babu alamun hakan zai faru a nan kusa,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

“Ko da hakan zai faru, babban kalubalen shi ne a shawo kansu domin su gudanar da sabon zabe a Nijar ta yadda za a mayar da jagorancin kasar hannun zababbiyar gwamnatin dimokuradiyya.”

Kamar yadda Dakta Hayatu ya bayyana, abu daya da ke kan teburin sulhu da sarakunan gargajiyan za su mika a matsayin bukatarsu ga sojojin ba wai batu ne na mika mulki ba, kamar yadda wasu suke zato.

Batu ne na ci gaba da tattaunawa da sojojin a siyasance da kuma shawo kansu domin gudanar da zabe daga baya.

TRT Afrika