Rikici tsakanin sojojin Sudan da rundunar RSF ya barke tun a watan Afrilu, inda dubbai suka rasu. Hoto/Reuters

Akalla mutum 43 suka rasu sakamakon hari da wani jirgi mara matuki ya kai a wata kasuwa da ke kudancin Khartoum babban birnin Sudan.

Ma’aikatan lafiya da masu gwagwarmaya sun bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da ake ba-ta-kashi tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF.

Sama da mutum 30 aka raunata a yayin wannan harin da aka kai a unguwar da lamarin ya faru, kamar yadda wata kungiyar ‘yan gwagwarmaya ta Resistance Committees da wasu ma’aikatan lafiya biyu da ke aiki a Asibitin Jami’ar Bashair suka shaida wanda a nan ake kula da wadanda suka samu raunuka.

Kungiyar gwagwarmayar ta wallafa bidiyo a shafinta na sada zumunta inda a bidiyon aka ga an nade gawarwaki a farin kyalle a harabar asibitin.

Babu tabbaci kan wane bangare ya kai harin jirgi mara matuki.

Sudan ta sha fama da yake-yake tun tsakiyar Afrilu bayan an samu rashin jituwa tsakanin sojojin kasar karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al Burhan da kuma Shugaban RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo.

Sama da mutum 4,000 wannan rikicin ya kashe, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da alkaluma a watan Agusta. Sai dai ana ganin adadin na asali ya fi haka, kamar yadda masu sharhi suke gani.

Sama da mutum miliyan biyar suka rasa muhallansu a cikin Sudan ko kuma suka gudu daga kasar, kamar yadda Hukumar Kula da 'Yan Ci-rani ta Duniya ta bayyana.

AP