Sojojin sun ce sun kai irin wannan harin a Jihar Zamfara inda suka kashe 'yan ta'adda. Hoto/NAF

Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta bayyana cewa ta kashe gomman ‘yan ta’adda bayan wani samame da jiragen samanta suka kai a maboyar ‘yan ta’addan.

Rundunar sojin ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi inda ta ce an kai wannan harin tare da hadin gwiwar dakarun Operation Hadin Kai da Hadarin Daji a wata sabuwar maboyar ‘yan ta’addan da ke Bukar Meram wanda ke kusa da Tafkin Chadi a Jihar Borno.

Mai magana da yawun sojin saman kasar Air Commodore Edward Gabkwet ya bayyana cewa an kai wa ‘yan ta’addan hari bayan an gano sun sauya matsuguni daga Suwa zuwa Bukar Meram wanda hakan zai iya sawa su rinka kai wa farar hula hari.

“Bayanan da aka samu bayan hare-hare ta sama sun nuna cewa an samu abin da ake so sakamakon an kashe ‘yan ta’adda da dama sannan an lalata babura sama da 40 da motocin girke bindiga shida, in ji shi.

Mista Gabkwet ya kuma ce sojojin sama na Operation Hadarin Daji sun kai irin wannan harin a ranar 11 ga watan Oktoba a yankin Sangeko da ke Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

A cewarsa, ‘yan ta’addan na Zamfara sun yi jerin-gwano kan babura kusan 70 a kan hanyar Kabaro zuwa Sangeko inda aka bude musu wuta tare da lalata musu babura da da kashe su da raunata wasu.

TRT Afrika