Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Nijeriya Zagon-Ƙasa wato EFCC ta nesanta kanta daga wani jerin sunaye wanda ke yawo a wasu jaridu da kafafen sada zumunta da ke cewa tana bincikar wasu tsofaffin gwamnoni kan zargin rashawa.
A ranar Asabar ne wani labari ya rinƙa yawo kan cewa akwai tsofaffin gwamnoni 58 waɗanda hukumar ke bincika kan zargin almundahana ta kimanin naira tiriliyan 2.187 a cikin sama da shekara 25.
Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC Dele Oyewale ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana rahotannin a matsayin na ƙarya.
Mista Oyewale ya bayyana cewa waɗanda suka ƙirƙiri jerin sunayen su kaɗai suka san manufar da suke son cimmawa.
“Hukumar EFCC, tana ganin ya zama wajibi ta nesanta kanta daga wani rahoto da ke yawo a kafafen watsa labarai na cewa ta fitar da cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnonin da ake bincike kan zargin cin hanci da rashawa.
“Rahoton mai taken: “EFCC ta saki cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnoni 58 da suka wawure tiriliyan N2.187”, a wata kafar watsa labarai, karya ne kuma hukumar ba ta fitar da wannan jerin sunayen ba ko kuma tattaunawa kan binciken tsoffin gwamnoni da wata kafar yada labarai,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sai dai a ƴan kwanakin da suka gabata hukumar ta EFCC ta yi ta bincikar wasu tsofaffin gwamnoni daga ciki har da tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello inda take zarginsa da cire dala miliyan 720 daga asusun jihar domin biyan kuɗin makarantar yaronsa.