Tun Fabrairun 2016 Jamus ke kula da sansanin sojin wanda har an taɓa lokacin da yake ɗauke da dakaru 3,200. / Hoto: Reuters

Sojojin Jamus a ranar Juma’a sun kammala janye dakarunsu daga Jamhuriyar Nijar.

Tun a ƙarshen watan Mayu, ƙasar ta Jamus ta cim ma matsaya da Nijar domin sahale wa sojojin na Jamus ɗin ci gaba da aiki da sansanin sojin samansu a Yamai babban birnin ƙasar har zuwa watan Agusta.

Sai dai tattaunawa domin ƙara wannan wa’adin ya ci tura, ganin cewa sansanin sojin ba zai ci gaba da samun kariyar gwamnatin ƙasar ba.

Manyan jami’an Nijar da na Jamus sun karanto wata sanarwa a ranar ta Juma’a domin sanar da kammala janye sojojin.

“Wannan yarjejeniyar ba tana nufin kawo ƙarshen yarjejeniyar soji tsakanin Nijar da Jamus ba, hasali ma ɓangarorin biyu za su ci gaba da ƙawance,” in ji su.

Jiragen ɗaukar kaya biyar ɗauke da sojojin Jamus 60 da kuma tan 146 na kayayyakin aiki sun sauka filin jirgi na Wunsdorf da ke Jamus a ranar Juma’a da misalin 6:30 agogon ƙasar inda suka samu tarbar sakataren harkokin tsaro na Jamus Nils Hilmer.

Tun Fabrairun 2016 Jamus ke kula da sansanin sojin wanda har an taɓa lokacin da yake ɗauke da dakaru 3,200.

Nijar na ƙarƙashin mulkin soji tun bayan da sojojin ƙasar ƙarƙashin Janar Abdourahamane Tiani suka yi wa Mohamed Bazoum juyin mulki, wanda a halin yanzu aka yi wa ɗaurin talala.

Sojojin na Nijar sun juya wa ƙasashen Yamma da ke ƙawance da Nijar ɗin baya daga ciki har da Faransa da Amurka inda suka karkata akalar ƙawancensu zuwa ga Rasha da Iran.

AFP