Hukumomi a Kenya sun tabbatar da cewa cutar haukan kare ko kuma rabies ne ya jawo kurayen kai harin / Photo: AA

Hukumar da ke kula da gandun dabbobi ta Kenya KWS, ta ƙaddamar da wani samame na musamman domin farautar wasu fusatattun kuraye waɗanda suka rinƙa kai muggan farmaki a yankin Juja da ke Kiambu.

Samamen na zuwa ne bayan wasu gungun kuraye sun halaka wani yaro ɗan shekara biyar da haihuwa a kwanakin baya. KWS ɗin ta bayyana cewa ta aika da jami’ai na musamman daga faɗin ƙasar domin farautar dabbobin.

“Mun aika da gomman jami’anmu daga sassa daban-daban na ƙasar. Suna da kayan aikin da suka dace domin farauta da kama kurayen,” in ji Joseph Dadacha, Babban Mataimakin Darakta na Tsaunin Central Rift da ke Kenya, kamar yadda ya bayyana a ranar Lahadi.

Zanga-zanga

Wannan lamarin ya jawo zanga-zanga, inda mazauna yankin suka rufe manyan tituna na tsawon sa’o’i a ranar Alhamis ɗin da ta gabata.

Hukumomin sun bayyana cewa da zarar an kama dabbobin, za a mayar da su wurare masu nisa daga inda jama’a ke zama.

Bugu da ƙari, dangane da wannan aikin samamen, hukumar ta ce za ta ci gaba da faɗaɗa aikinta na sinitiri tare da aiwatar da shirye-shiryen wayar da kai da kuma haɗa kai da jama’ar da ke zaune a yankunan, don guje wa afkuwar irin haka a nan gaba.

Haka kuma hukumar da ke kula da muhalli ta ƙasar ita ma za ta rinƙa saka ido kan wuraren da ake jefar da bola da haƙar dutse domin magance matsalolin muhalli waɗanda ke haddasa hakan.

A watan Fabrairun bana, hukumar da ke kula da gandun dabbobi ta Kenya KWS ta tabbatar da cewa cutar rabies ce ta rinƙa jawo kuraye na far wa jama’a a yankunan Kajiado da Kiambu.

TRT Afrika da abokan hulda