Rahotanni daga Nijeriya na cewa jam’iyyar adawa ta PDP a kasar ta sauke shugabanta, Iyorchia Ayu, bayan umurnin wata kotu.
A wani taron manema labaran da ya kira a babban ofishin jam’iyyar a Abuja, sakataren watsa labaran jam’iyyar Debo Ologunagba, ya ce bayan nazari kan umarnin kotu ne sai kwamitin amittattun jam’iyyar ya yanke shawarar sauya shugaban jam’iyyar.
Ya kara da cewa Ambasada Umar Iliya Damagum, wanda ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar a arewacin kasar shi ne sabon shugaban PDP da zai maye gurbin Iyorchia Ayu.
Cire Iyorchia Ayu din dai ya kasance daya daga cikin bukatun da gwamnoni biyar na jam’iyyar suka bayar idan har ana so su bai wa jam’iyyar goyon baya a zaben shugaban kasar da ya gabata.
Gwamnonin da suka hada da Nyesom Wike na jihar Ribas da Seyi Makinde na jihar Oyo da Okezie Ipkeazu na jihar Abia da Samuel Ortom na jihar Binuwe da kuma Infeanyi Ugwuanyi na jihar Inugu, ba su ce komai ba tukunna game da cire shugaban da jam’iyyar ta yi.
Jam’iyyar dai ba ta yi nasara a zaben shugaban kasar da aka yi a watan Fabrairu ba.
Masu sharhi da dama na ganin rarrabuwar kan da aka samu a jam'iyyar sakamakon rashin cire Ayu na daga abubuwan da suka jawo mata faduwa a zaben shugaban kasar.