Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Nijar ya musanta rahotannin da ke cewa wasu bata-gari sun kona ofishin jakadancin kasar da ke Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Jakadan Nijeriya a Nijar, Ambasada Mohammed Sani Usman, ya bayyana haka ne a hira da TRT Afirka ranar Juma'a.
Ya ce wani bidoyi da ake watsawa a shafukan sada zumunta da ke nuna wani wuri - da aka ce ofishin jakadancin Nijeriya a Nijar ne yana ci da wuta - na bogi ne.
Sai dai ya ce an kara jami'an tsaro a ofishin jakadancin saboda gudun abin da ka je ya komo.
''A halin da ake ciki, gwamnatin Nijeriya ta karo mana jami'an tsaro don tabbatar da lafiya da tsaron duk wani dan Nijeriya da ke Nijar,'' in ji shi.
A ranar Alhamis ne aka rika watsa wani bidiyo a shafukan sada zumunta da ke nuna wani wuri da aka ce ofishin jakadancin Nijeriya a Yamai ne yana ci da wuta.
Lamarin na faruwa ne a yayin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta umarci dakarunta su daura damarar tunkarar sojojin da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a karshen watan jiya.
Shugaban ECOWAS wanda kuma shi ne shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce sun dauki matakin ne bayan sojojin sun yi fatali da umarni da kungiyar ta ba su na mayar da Bazoum kan mulki cikin mako guda.
Sojojin sun ce za su mayar da martani mai karfi kuma cikin "gaggawa" kan duk wata barazana da za a yi musu daga kasashen waje.
Hasalima sun janye jakadun Nijar daga Nijeriya da Amurka da Faransa da kuma Togo.
Kazalika sun rufe sararin samaniyar kasar bayan da suka yi zargin cewa ana shirin kai musu hari.