Shugaba Bola Tinubu ba ya fargaba kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben Nijeriya za ta yanke domin yana da yakini shi ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023, a cewar fadarsa.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV ranar Litinin da maraice.
An gudanar da zaben shugaban kasar ne a watan Fabrairu kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 37 na kuri'un da aka kada.
Labari mai alaka: Zaben Nijeriya na 2023: An soma shari'a kan zaben da ya bai wa Bola Tinubu nasara
Dan takarar da ke biye masa shi ne Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya samu kashi 29 yayin da dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi ya samu kashi 25.
Sai dai Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu 'yan takarar sun garzaya kotu inda suke kalubalantar zaben.
A ranar Laraba ake sa ran kotun za ta yanke hukunci game da zaben a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya yi balaguro zuwa India domin halartar taron kungiyar kasashen G20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya.
'Muna da kwararrun lauyoyi'
Da yake mayar da martani kan tambayar da aka yi masa cewa, shin Shugaba Tinubu ba ya fargabar shan kaye a hukuncin da kotun za ta yanke a daidai lokacin da ya bar kasar, Mr Ngelale ya ce "(Shugaba Tinubu) bai damu ba domin kuwa ya yi amannar shi ya ci zaben (shugaban kasa)."
"Mun yi amannar cewa mun gabatar da kwararan hujjoji, mun yi amannar cewa muna da shaidu, mun yi imani cewa muna da tawagar lauyoyi mafi hazaka a kasar nan da ke rike da hujjoji mafi inganci...hakikanin gaskiya mun ci zabe a mafi yawan sassan Nijeriya," in ji shi.
Sai dai kakakin shugaban na Nijeriya ya kara da cewa duk yadda sakamakon hukuncin kotun ya kaya, Shugaba Tinubu zai ci gaba da tabbatar da cewa an mutunta hukumomin kasar.