Ma'aikatar Harkokin Wajen Ivory Coast ta ce gwamnatin ƙasar a ranar Asabar ta fitar da jakadanta da jami'an diflomasiyya da kuma 'yan kasar da dama daga kasar Lebanon saboda karuwar rikici a yankin.
Ma'aikatar ta bayyana cewa ta kwashe kimanin mutum 100 ‘yan ƙasar ta Ivory Coast waɗanda kusan 60 daga cikinsu sun bayyana cewa suna so su bar ƙasar domin raɗin kansu.
Ma'aikatar ta ce ƙasar ta Ivory Coast ta shirya aikin kwashe ‘yan ƙasar daga Lebanon ne saboda tashin hankali tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hezbollah.
Kusan mutum 20 sun bar ƙasar haka kuma za a ƙara kwasar ƙarin wasu idan aka samu gurbi a jiragen kasuwa, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta ƙara da cewa.
Zuwa yanzu dai, sama da mutum 2,653 Isra’ilar ta kashe a Lebanon tun bayan soma wannan yaƙin.