Inès Ngounga a yanzu tana da kwastamomi da dama daga faɗin duniya daga lemon da take haɗawa. / Hoto: TRT Afrika

Jajayen furanni da ke fitowa a jikin yakuwa, wanda tsiro ne da ya yi suna a Yammacin Afirka, na ɗauke da wasu abubuwa masu kauri da ke fitowa a samansa waɗanda ke samar da abubuwan mamaki

Kamar yadda kamshi da kuma ɗanɗanon ganyensa yake, haka lemun da ake samu ƙasashen nahiyar waɗanda suka haɗa da Guinea da Congo da Kenya da Gabon da Senegal.

Hanyar da Inès Ngounga ta ɗauka domin neman kuɗi ta samo asali ne bayan ta soma bincike kan irin bunƙasar da ke tattare da yakuwa, wadda za a iya samu a kowane lokaci.

Zoɓo shi ne lemo mai ƙara lafiya wanda ya yi suna, sai dai Inès ta yi amfani da basirarta domin haɗawa da farin zoɓo wanda take ganin ɗan uwan jan ne.

Lemon wanda ake taƙama da shi a wasu sassan Afirka na da wani ɗanɗano na daban. / Hoto: TRT Afrika

Matashiyar wadda asalinta ƴar kudancin Gabon ce, na ganin za a iya mayar da zoɓo wata haja da za a iya sayarwa a faɗin duniya.

"Na soma yin gwaji ne da ɗanɗano mai ƙamshi daban-daban a gida inda na riƙa bayar da lemon ga baƙi, na kasance ina sayar da zobo ko bukulu ga abokan aikina, wanda sunansa ne da harshen ƙasar Gabon," kamar yadda Inès ta shaida wa TRT Afrika.

Ta ƙaddamar da sana'arta a 2016, inda ta soma da jarin CFA 10,000, (kusan dala 16.45 kenan) bayan ta shafe shekaru tana neman aikin yi wanda zai yi daidai da digirin da take da shi na biyu.

Kamfanin da na soma ba tare da nazarin kasuwarsa ba, a halin yanzu ya haɓaka matuƙa.

"Ana kiran bukulu da bissap. A lokacin wani taron baje-koli, wani kwastoma ya bayar da shawara kan na ɗauki 'bissap na Gabon'. Na zaɓi bukulu bayan duba abubuwa da dama, wanda suna ne da ke nufin yakuwa da harshen Punu wanda harshe ne da ake magana da shi a kudancin Gabon," kamar yadda Inès ta bayyana.

Inès na haɗawa da kankana da abarba da sauran kayan itatuwa domin samun ɗanɗano mai daɗi. / Hoto: TRT Afrika

Amfani ga lafiya

Yakuwa na ɗauke da sinadarin iodine matuƙa, inda ta yi suna a faɗin Afirka. Jamaica da Mexico na daga cikin ƙasashen da suka fi amfani da ita a wajen nahiyar.

A cewar gidauniyar Louis Bonduelle, wacce ta mayar da hankali kan tasiri mai dorewa a ɓangaren cin abinci ta hanyar tabbatar da kowa yana amfani da kayan lambu cikin abincinsa, ta bayyana cewa yakuwa na maye gishirin jiki.

Gidauniyar ta bayyana cewa zoɓo ba lemo ne wanda yake da sinadaren calorie mai yawa ba, inda ta ce yana ɗauke da vitamin B9 mai yawa, kuma masu farfaɗowa daga rashin lafiya yana da kyau su sha shi.

Haka kuma gidauniyar ta bayyana cewa zobon na samar da vitamin C da sinadaren iron da magnesium da postassium waɗanda ke taimaka wa jiki da jini.

Haka kuma ganyen shi ma yana ɗauke da sinadarin calcium.

Yakuwa na daga cikin abincin da Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da shawara kan a ci.

Yadda ake haɗa lemo

Inès ta yanke shawarar yin zoɓo amma fari bayan ta karanta kan batun.

"Yana magana kan farin bukulu. Jan zoɓo kaɗai na sani a lokacin. Sai na je wurin mai kawo mani zoɓo inda na tambaye shi ko yana da fari, daga nan aka fara," kamar yadda ta tuna.

Kamfaninta ya ƙaddamar da farin bukulu a 2018, inda kwastamomi suka nuna jin daɗinsu.

Launin zoɓon ya danganta da yadda yake a lokacin da aka tsinko shi. / Hoto: TRT Afrika

Tsintar ganyen zoɓo mai kyau yana daga cikin hanyoyi mafi muhimmanci a wurin haɗa shi. Da zarar an kammala hakan, an wanke shi domin ya bushe.

"Mataki na gaba shi ne a cika ƙatuwar tukunya da ruwa, ya kuma danganta da adadin da za a dafa. Ana dora tukunyar a kan wuta bayan an zuba zoɓo da na'ana'a, sai a dafa na tsawon awa guda sai a bar shi ya kwanta," kamar yadda Inès ta shaida wa TRT Afrika.

Bayan nan ana tace shi sai a ware shi daga dafaffen ta hanyar amfani da rariya ko kuma abin tata domin a matse.

Matakai na ƙarshe su ne saka sukari a ciki da kayan ƙanshi sai kuma sakawa a kwalabe.

Inès na aiki tuƙuru a kowane lokaci domin inganta lemon da take sayarwa. " Na soma sana'ar ne da kwalaben roba, sai da na shafe shekara biyar sannan na samu kwalabena na kaina, ina godiya ga mai kawo mani su daga ƙasar waje," kamar yadda ta bayyana.

TRT Afrika