Sojojin sun bayyana kwace mulki ne sa'o'i bayan fitar da sakamakon zaben shugaban kasa.

Wasu manyan sojoji a Gabon sun bayyana a gidan talabijin na kasar da sanyin safiyar ranar Laraba inda suka yi ikirarin kifar da gwamnatin kasar.

Sun bayar da sanarwar ce sa'o'i kadan bayan hukumar zaben kasar ta fitar da sakamakon zaben shugaban kasar wanda ya nuna cewa Shugaba Ali Bongo ya yi nasara da kashi 64.27.

Yayin da suke jawabi a gidan talabijin na Gabon 24, sojojin sun ce sun soke zaben kasar.

Labari mai alaka: Ali Bongo Ondimba ya sake yin nasara a zaben shugaban kasar Gabon

"A yau, 30 ga watan Agusta, 2023, mu jami'in tsaro na hadin-kai na Committee for the Transition and Restoration of Institutions (CTRI), a madadin al'ummar Gabon da masu kare hukumomi, mun yanke shawarar kare zaman lafiya ta hanyar kawo karshen wannan gwamnati," a cewar kakakin sojojin.

Ya kara da cewa an rufe iyakokin kasar har "sai abin da hali ya yi."

Kawo yanzu gwamnatin kasar ba ta ce komai game da ikirarin sojojin ba.

Sai dai Firaiministar Faransa Elisabeth Borne ta ce suna sanya ido a kan abin da ke faruwa a Gabon bisa 'matukar kulawa'.

Ita ma China ta ce tana "sanya ido sosai kan halin da ake ciki" a Gabon sannan ta yi kira da a "tabbatar" da tsaron lafiyar iyalan Bongo.

Idan juyin mulkin ya tabbata, ya kawo karshen fiye da shekara 50 na mulkin da iyalan Bongo suka kwashe suna yi a kasar, wanda mahaifinsa ya soma.

Kazalika zai kasance juyin mulki na takwas da aka yi a Yammaci da Tsakiyar Afirka tun daga 2020. Tuni dai aka yi juyin mulki a kasashen Mali, Guinea, Burkina Faso, Chadi da Nijar.

Rahotanni sun ce an yi ta jin karar harbe-harben bindigogi a Libreville, babban birnin na Gabon da sanyin safiyar Laraba.

Tun da farko, hukumar zaben kasar ta ce Ali Bongo ya yi nasarar yin ta-zarce karo na uku.

Babban abokin hamayyarsa Albert Ondo Ossa, ya samu kashi 30.77 yayin da sauran 'yan takara 12 suka samu sauran kuri'in, in ji shugaban hukumar zaben Michel Stephane Bonda.

TRT Afrika