Gwamnatin kasar ta sanar da rufe iyakokin kasar na ruwa da kan tudu daga sha biyu na dare na ranar Juma'a zuwa Asabar sha biyu na dare. Hoto/AA

Daga Jean-Rovys Dabany

A ranar Asabar 26 ga watan Agusta ne ake gudanar da zabe a kasar Gabon wadda ke a tsakiyar Afirka. Kasar wadda rainon Faransa ce na da mutum miliyan 2.3 inda kusan mutum 19 ke takarar shugaban kasa a kasar.

Haka kuma ana sa ran masu zaben za su zabi ‘yan majalisa da kuma shugabannin kananan hukumomi.

Akwai kusan mutum 800,000 da suka cancanci su jefa kuri’a a kasar inda akasarinsu matasa ne.

Shugaba Ali Bongo Ondima ya jagoranci kasar har wa’adi na biyu inda ake shekara bakwai a kowane wa’adi inda ya gaji mahaifinsa.

A halin yanzu yana neman wa’adi na uku bayan wani sauyi da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar ya ba shi damar nema sabon wa’adin.

Wanda zai kara da shi a wannan karon shi ne Albert Ondo Ossa, wanda ya kasance tsohon minista kuma farfesa a kan harkar tattalin arziki inda kuma yake da goyon bayan ‘yan takara shida a cikin 19 na kasar.

A kasar da kusan kashi 60 cikin 100 matasa ne kuma ba su da aikin yi, duka ‘yan takarar na yin manyan alkawura dangane da matasan domin samun nasara a zaben.

Cedric Wandja mai shekara 38, na wakiltar irin masu zaben da ‘yan takarar ke mayar da hankali a kansu wato matasa kenan. Ya taba mafarkin aikin ofis amma hakan ba gaskiya bane.

A yayin da yake jiran kwastamomi cikin hakuri a shagonsa da ke kasar Mont-Bouet, wadda ita ce mafi girma a Libreville babban birnin Gabon, Cedric yana tuna lokacin da ya bata shekara takwas yana neman aiki bayan kammala karatunsa.

Ya kamata da ya je jami’a a lokacin amma ba shi da kudin da zai iya zuwa.

Kudi masu yawa

Domin tallafa wa iyalinsa, sai Cedric ya kafa shago a Mont-Bouet, inda yake sayar da kayayyaki da takalma.

Shagon na samar masa da akalla CFA 400,000 wato kimanin dala 800 a duk wata.

Kusan kashi 60 cikin 100 na matasan da ke Gabon ba su da aikin yi. Hoto/AA

Cedric na kallon kasuwanci a matsayin wata hanya daya da za ta taimaki matasan gabon da dama da ba su da aikin yi.

“Akwai da dama daga cikinmu wadanda suka fahimci kasuwanci zai iya samar mana da abinci ga iyalanmu, haka kuma wata hanya ce ta samar da babban kasuwanci a wani mataki,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Ga kasar da ba ta da mutane da yawa da kuma albarkatun kasa kamar sauran kasashen da ke da girmanta, rashin aikin yin matasa idan ya zarce kashi 30 cikin 100 ya zama babban kalubale.

A wasu bayanai da ke kunshe a cikin wani rahoto da Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya IMF ta wallafa a bara ya jaddada cewa matakin talauci da rashin aikin yi a Gabon na da yawa duk da kasar na da albarkatun kasa wadanda suka hada da mai da zinare da manganese.

A fadin Libreville, akwai mutane irin su Cedric da ke rayuwar da ya kamata ta fi haka. Akwai da dama wadanda suka kammala karatu; wasu sun soma sana’o’i inda wasu kuma sun soma kananan ayyuka ko kuma suna samun abin kashewa a wasu ‘yan ayyuka da suke yi.

Eric Etoung, wanda ke sana’ar aski, yana ganin akwai bukatar gwamnati ta kara bayar da muhimmanci ga bangaren sana’o’i da kasuwanci domin ba jama’a damar samun ayyuka.

"Wannan ba karamin abu bane, hakika, amma kowa yana tunanin yin aiki a ofis shine abin da zai dace da kowa, alhalin ba shine kadai mafita ba," in ji shi.

Yakin neman zaben da aka yi gwagwarmaya

Kilomita daya daga wurin da Eric ke tsaye, a daya daga cikin titunan da suka fi hada-hadar jama’a a babban birnin kasar, Joel mai shekara 29 ya je domin ya halarci gangamin yakin neman zabe wanda jam’iyyar da ke nuna goyon bayanta ga Ondo Ossa ta shirya.

Babban abokin adawa, Albert Ondo Ossa na da goyon bayan 'yan takara shida cikin 19. Hoto/Reuters

A 2009, ya zabi Shugaba Ali Bongo, wanda a gare shi, ya kasance wanda mutane ke yi wa kyakyawan zato.

Bayan shekara 14 kuma bayan wa’adi biyu, ya yi takaici kan rashin cika alkawuran da dan takarar ya ki yi wa matasa.

Joel ya fito karara ya bayyana cewa ya sauya bangaren da yake yi wa biyayya zuwa bangaren adawa, akalla zuwa yanzu.

“’Yan Gabon sun gaji da alkawuran karya. Samun kudin da za su isa a sayi abubuwan bukatun yau da kullum kamar abinci na kara wuya. Muna bukatar sauyi,” kamar yadda ya bayyana kafin ya shiga cikin jerin abokansa wadanda suka je su shiga gangamin yakin neman zaben na ‘yan adawa.

Kusan makonni biyu da suka gabata kafin zabe, Shugaba Ali Bongo ya gudanar da gagarumin yakin neman zabe wanda ya jawo jama’a. Hotunansa duk sun mamaye manyan hanyoyin babban birnin.

Ali Bongo na neman wa'adi na uku na shugaban kasa bayan an sauya kundin tsarin mulkin kasar. Hoto/Reuters

Germaine, wanda magoyin bayan Ali Bongo ne, ya ce shi ne “shugaban kasar da ya fi” kuma shi ne dan takarar da ya fi dacewa da kujerar a karo na uku.

“Muna son shugaban da ke neman zaman lafiya ga mutane. Ba mu son shugabannin da ke yunwar mulki,” kamar yadda matashin mai zaben ya bayyana.

A makon da ya gabata, ‘yan adawar sun taru a kusa da Alternance 2023, wanda hadaka ce da ke goyon bayan babban abokin adawar Shugaba Ali Bongo.

Taron ya nuna goyon bayansa ga Ondo Ossa a matsayin dan takarar da suka amincewa mawa.

Haka kuma akwai tsoffin ministoci uku wadanda suke goyon bayansa: Alexandre Barro Chambier na Rassemblement pour la Patrie et la Modernité da Paulette Missambo ta National Union da kuma Raymond Ndong Sima wanda ya kasance Firaiminista na kasa da shekaru biyu a karon farko na mulkin shugaba Ali Bongo.

'Yan Gabon kamar Cedric da suka tafi jefa kuri'a, na da burin ganin wadanda aka zaba za su gyara tattalin arzikin kasar da kuma samar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

TRT Afrika