A ranar 15 ga watan Afrilu hukumar INEC ta ce za a kammala sauran zabukan da suka rage Photo/AA

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC ta sanar da ranar Asabar 15 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a kammala zabukan da suka yi kwantai da ba a kammala ba a babban zaben 2023.

A wata sanarwa da INEC din ta fitar, ta ce za a karasa zabukan gwamnoni a jihohin Adamawa da Kebbi, sannan akwai zaben sanatoci biyar da na ‘yan majalisar wakilai 31 sai na ‘yan majalisar jihohi 58.

Hukumar ta tabbatar da cewa musamman a zaben ‘yan majalisar da za a gudanar, za a gudanar da zabukan ne a rumfunan zabe kalilan.

Sannan hukumar ta bayyana cewa za ta wallafa cikakkun bayanai a shafinta na intanet game da jerin rumfunan zabe daga jihohi zuwa kananan hukumomi da wuraren rajistar zabe, da kuma adadin katin zabe da aka karba kafin ko a ranar Laraba 28 ga watan Maris din 2023.

Hukumar zaben ta bukaci jam’iyyu da ‘yan takara da masu ruwa da tsaki da su kula da rana da kuma wuraren da za a gudanar da zaben.

Sannan INEC din ta bukaci jam’iyyu da ‘yan takara da magoya bayansu da su kalli wannan lamari a matsayin zabe ba yaki ba.

An dai kammala zaben gwamnoni 26 da ‘yan majalisar dattijai 104 sai na wakilai 329 da kuma ‘yan majalisar jihohi 935, kuma tuni aka sanar da wadanda suka lashe zaben.

A jihohin da za a kammala zabe musamman jihar Adamawa, za a kara ne tsakanin Ahmadu Umaru Fintiri na Jam’iyyar PDP sai kuma Aishatu Dahiru Binani ta Jam’iyyar APC.

Sannan a jihar Kebbi kuwa za a kara ne tsakanin Alhaji Nasiru Idris na Jam’iyyar APC da kuma Manjo Janar Aminu Bande (mai ritaya) na Jam’iyyar PDP.

TRT Afrika