Kotun sauraron korafin zabe a Nijeriya na 2023, wadda ke zamanta a Jihar Kano ta soke zaben dan majalisar wakilai na tarayya na karamar hukumar Tarauni dan jam'iyyar NNPP, inda ta ayyana dan takarar APC a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Rahotanni daga zauren kotu sun nuna cewa kotun ta ba da umarni na karbe shaidar lashe zabe daga wajen dan majalisa mai ci, Muktar Umar Yarima, na jam'iyyar NNPP, sannan a mayar wa Hafizu Kawu na jam'iyyar APC.
Tun da fari, Hafizu Kawu wanda shi ne tsohon dan majalisa mai wakiltar Tarauni, wanda ya sha kaye a zaben, ya shigar da korafin cewa Mukhtar Yarima ya gabatar wa hukumar zabe ta INEC shaidar kammala karatun firamare ta bogi.
Kotun zaben ta samu jagorancin Mai Shari'a I.P. Chima, kuma tawagar alkalan ta bayyana cewa Yarima bai cancanci tsayawa takarar ba, saboda haka jam'iyyar NNPP ba ta da dan takara a zaben da ya gudana a watan Fabrairu.
Kotun ta ki amincewa da uzurin Yarima na cewa ya sauya sunayensa a shekarar 2022, saboda yana amfani da suna uku "Umar Mukhtar Zakari" a fasfo dinsa, tun shekarar 2009, bayan shaidar firamere dinsa ta ce sunansa "Umar Mukhtar".
Lauyan Mukhtar Umar Zakari, mai suna Barista Rabiu Sadik, ya shaida wa TRT Afrika cewa, "Za mu daukaka kara, kasancewar mun gabatar da hujjoji har daga shugaban makarantar Hausawa Primary School, mai nuna cewa Mukhtar ya yi karatu a can".
Shi kuwa Barista Abubakar Nuhu, daya daga cikin lauyoyin Hafizu Kawu ya ce, "Madogararmu ita ce Umar Mukhtar ba shi da halattattun takardu da zai yi takara da su, kuma mun gabatar da hujjoji gaban kotu kuma kotu ta gamsu da su."