Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce za ta sanya kafar wando daya da masu neman tayar da zaune tsaye. / Hoto: Reuters

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce ta karfafa tsaro a fadin kasar gabanin hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa za ta yanke ranar Laraba.

Kakakin rundunar 'yan sandan Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Talata.

"A yunkurin tabbatar da tsaro da dakile karya doka da oda a fadin kasa sakamakon hukuncin da kotun sauraren karar zaben shugaban kasa za ta yi ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, rundunar 'yan sandan Nijeriya ta karfafa tsaro sannan ta aike da karin jami'ai a fadin Nijeriya," in ji sanarwar.

Adejobi ya gargadi masu neman tayar da zaune tsaye yayin yanke hukuncin zaben da su shafa wa kansu lafiya domin kuwa "rundunar 'yan sanda ba za ta amince da duk wani abu da zai haddasa rikici ba".

A ranar Litinin shugaba Bola Tinubu ya ce ba ya fargaba kan hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben Nijeriya za ta yanke domin yana da yakini shi ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 2023.

Mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV .

Labari mai alaka: Zaben Nijeriya na 2023: 'Tinubu ba ya fargaba kan hukuncin da kotun zabe za ta yanke'

An gudanar da zaben shugaban kasar ne a watan Fabrairu kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya, INEC, ta ayyana dan takarar jam'iyyar APC Bola Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara da kashi 37 na kuri'un da aka kada.

Dan takarar da ke biye masa shi ne Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya samu kashi 29 yayin da dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi ya samu kashi 25.

Sai dai Atiku Abubakar, Peter Obi da wasu 'yan takarar sun garzaya kotu inda suke kalubalantar zaben.

TRT Afrika