Baya daga asarar rayuka da dumbin dukiya da jikkatar mutane, yaki yana kuma yin mummunan tasiri a wajen da aka yi shi / Hoto: AP

Daga Shamsiyya Hamza Ibrahim

Yaki mummunan abu ne da babu wanda zai so ya ga faruwarsa ko a inda yake ko ma a wani wajen daban.

Baya ga yakin da ake yi a Ukraine da Habasha, yanzu kuma yaki ya barke a Sudan tsakanin sojojin gwamnati masu biyayya ga Shugaba Abdul Fattah Al Burhan da kuma dakarun rundunar RSF da ba ta gwamnati ba da Janar Mohammed Hamdan Daglo ke jagoranta.

Sai dai wannan yaki, ga dukkan alamu zai iya jawo wasu manyan matsaloli ga kasar da ma makwabtanta a nahiyar Afirka, wacce dama take ta fafutukar shawo kan wasu matsalolin da suka addabe ta.

Baya daga asarar rayuka da dumbin dukiya da jikkatar mutane, yakin yana kuma yin mummunan tasiri a wajen da aka yi shi.

Ga dai jerin wasu matsaloli da yakin ka iya haifarwa:

1. Fargabar makwabtan Sudan

Sudan ce kasa ta uku mafi girman fadin kasa a nahiyar Afirka, wadda kuma take da iyaka da Kogin Nilu da ke da muhimmanci ga kasashen Masar da Habasha da suke makwabtaka da ita.

Sauran kasashen da Sudan ta yi iyaka da su ne Libya da Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Eritiriya da Sudan ta Kudu, wadda ta balle daga Sudan a 2011.

A hirar da TRT Afrika ta yi da tsohon jakadan Nijeriya a Sudan, Sulaiman Dahiru, ya bayyana cewa yawancin kasashen da ke makwabtaka da Sudan su za su fi shan wahala a rikicin da ya mamaye kasar.

"Abin damuwar shi ne dama yawancin kasashen da ke kusa da Sudan na fama da nasu matsalolin tsaron da suka hada da hare-haren masu ikirarin jihadi ko kuma kungiyoyin ‘yan tawaye da suke kai-kawo a duk lokacin da suka ga dama a kan iyakokin kasashen, yanzu wannan matsala za ta ta'azzara wadannan matsaloli,’’ in ji Ambasada Dahiru.

2. Kwararar 'yan gudun hijira

Kamar yadda aka sani duk kasar da ta tsinci kanta a cikin yaki to akwai yiwuwar kwararar 'yan gudun hijira zuwa wasu kasashen.

Don haka ko a wannan lamari na Sudan ma, kwararru na ganin rikicin zai haifar da karin 'yan gudun hijira daga Sudan.

Ya zuwa watan Satumban 2022, Habasha da ke da yawan al'umma a yankin, tana da mutum sama da miliyan biyu da suka rasa matsugunansu sakamakon rikici tsakanin gwamnatin tarayyar kasar da kungiyar 'yan tawayen TPLF da ke mulkin yankin Tigray.

Har ila yau Habasha na karbar 'yan gudun hijira kusan miliyan guda daga Sudan da kuma Sudan ta Kudu da Somaliya da Eritiriya da Chadi.

"A halin da ake ciki rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 20,000 ne suka fita daga Sudan zuwa wasu kasashen da ke da makwabtaka,’’ a cewar wani masanin harkokin diflomasiyya, Abduhakeem Garba Funtua.

Ministan Yada Labarai kuma mai magana da yawun gwamnatin kasar Chadi Aziz Mahamat Saleh, ya shaida wa manema labarai cewa an bude kofa ga mutane sama da 20,000 musamman a yankin Assoungha na lardin Quaddai ‘’a kullum mutane suna shiga kuma an bude kofofin ba da agaji."

Mutane na ta ficewa daga Sudan don yin gudun hijira/ Hoto: AA

3. Bazuwar Makamai

Bazuwar makamai matsala ce da za a iya cewa za ta yi mummunan tasiri a kan yankuna ko kasashen da ke zagaye da inda rikici ya barke.

An ga irin haka ta faru bayan rikicin Libiya da ya yi sanadin hambarar da dadadden shugaban kasar Mu'ammar Ghaddafi, inda masana da hukumomi suka tabbatar da cewa lamarin ya jawo bazuwar makamai sosai a kasashen Afirka.

Abdulhakeem Garba ya shaida wa TRT Afirka cewa "babu wani cikakken tsaro a kan iyakokin da suka hada kasar Sudan da sauran kasashe fiye da biyar da suke makwabtaka.

"Don haka idan ba a gaggauta kawo karshen rikicin kasar ba, za a iya samun karin wasu kungiyoyi da bazuwar makamai lamarin da zai kara yin illa ga kasar da sauran kasashe da ke kewaye da ita.

"Kuma hakan zai iya zama dandali na 'yan ta'adda kuma za a iya shafe tsawon shekaru ana yaki a kasar."

Yakin da aka yi a Libya ya sa makamai sun watsu a Afirka don haka masana na ganin rikicin Sudan ka iya ta'azzara matsalar

4. Rushewar tsarin ilimi

Daya daga cikin abubuwan da ke kawo wa kasashe irin Sudan ci gaba shi ne bangaren ilimi ta yadda ake samun dalibai daga kasashen waje musamman na Afirka da ke zuwa kasar neman ilimi.

Hakan yana karfafa tattalin arzikinta da kai mata ci gaba. Sai dai kwararru na ganin rikicin da ake fama da shi a yanzu zai kawo tsaiko da matsala a fannin, musamman ma daliban kasashen waje.

Duk da cewar babu takaimaiman adadin daliban kasashen ketaren da ke karatu a Sudan, masu bibiyar al'amura a kasar sun yi kiyasin cewar sai dai a kwatanta adadin daliban da baki, la’akari da cewar adadinsu na iya kai wa dubbai.

Daliban da dama sun yi ta neman a kai musu dauki ta hanyar wallafa sakonni a shafukan sada zumunta.

Tuni hukumomin wasu kasashen Afirka da ke da dalibai a Sudan suka fara kwashe al'ummarsu ciki har da daliban, sai dai babu tabbas a kan sanin makomar karatunsu.

Amma ga alama karshen karatun wasu daliban ya zo kenan ko kuma a sauya musu wajen yin karatun, kamar yadda wani dan Nijeriya ya shaida min cewa har ya fara tunanin inda zai mayar da 'ya'yansa da ke karatu a kasar.

Nijeriya kadai na da sama da mutum 10,000 da ke karatu a Sudan, a halin da ake ciki Allah kadai yasan yadda za a magance rikicin sudan," in ji Abdulhakeem.

5. Yunwa da cututtuka

Yaki kan zo da mummunan tasiri na karanci da rashin abinci a yankin da ake yin sa, ta yadda sai dai mutane su dinga dogara da kayayyaki daga kungiyoyin agaji na duniya don su rayu.

A lamarin rikicin Sudan ma, tuni an fara kai wa wannan matakin. Kuma shi kansa rabon kayan agajin yana cin karo da matsaloli a yanzu haka, ta yadda hukumomin da ke rabawan suka ce ana sacewa.

Kazalika batun yaduwar cututtuka ma wani abu ne da ake samu a lokutan yaki.

Yanzu haka a Sudan, cibiyoyin lafiya duk sun durkushe saboda rashin kayayyakin kula da majinyata. Hasalima Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa kawo yanzu an rufe kashi 60 cikin dari na asibitoci da cibiyoyin lafiya na Khartoum, babban birnin Sudan. Ko ba a fada an san cewa hakan na kara tabarbarar da tsarin kiwon lafiya.

Sannan akwai cututtukan da kan bazu a lokutan yaki irin su amai da gudawa da zazzabin maleriya da sauran su, wadanda masana ke fargabar ana iya samun barkewar su a Sudan.

TRT Afrika