Daga Brian Okoth
Ibrahim Traore shi ne shugaban Burkina Faso a yau, bayan juyin mulki biyu a kasa da wata tara – watan Janairu zuwa Satumbar 2022.
Traore ya ce sun cire Damiba daga mulki ne saboda ya kasa shawo kan matsalar rikicin masu tayar da kayar baya, kamar yadda ya bayyana a wani jawabi da ya yi a talabijin a ranar 1 ga watan Oktoban 2022.
Ya zama shugaba mafi karancin shekaru a fadin duniya a watan Satumba, lokacin da shi da wasu kananan hafsoshin soji suka hambarar da Laftanal Kanal Paul Henri Damiba, wanda shi ma ya hau kan karagar mulkin ne ta hanyar juyin mulki a watan Janairu.
Har sai a ranar 30 ga watan Satumbar shekarar 2022, ba a san Traore ba sosai, musamman a fadin kasar Burkina Faso.
Traore ne ya kifar da gwamnatin Damiba, mai shekara 41, wanda yake kasa da shi da shekara bakwai a aikin soja, kuma yake kasa da shi ta fuskar mukami a rundunar sojin kasar.
Karin girma cikin sauri
A tsarin mukami a rundunar sojin, Traore yana rike da mukamin Capitaine ne, wato mukamin kyaftin kenan a harshen Faransanci.
Akwai mukamai uku da ke gaban kyaftin. Su ne Kwamanda da Laftanal Kanal da kuma Kanal. Burkina Faso ta dauki irin salon mukaman da ake da su ne a rundunar sojin Faransa, kasancewar Faransa ce ta yi mata mulkin mallaka.
Mutane da yawa suna bbayyana Traore da wanda ya samu karin girma cikin sauri a aikin soja.
Bayan ya yi aiki a matsayin karamin hafsan soja a rundunar sojin Burkina Faso, Traore ya fara samun daukaka ne a shekarar 2014, yayin da aka tura shi aiki kasar Mali a matsayin soja karkashin shirin samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya (MINUSMA).
Wasu sojoji a rundunar sojin Burkina Faso sun shaida wa gidan rediyon Radio Omega cewa lokacin da aka tura Traore Mali "ya nuna basira."
Lokacin yana da shekara 26, Traore ya "tsalle tarkon" da mayaka masu ikirarin kishin addini suka dana masa a arewacin Timbuktu, kamar yada wani da ba ya so a bayyana sunansa ya shaida wa Radio Omega.
Kwarewa wajen shugabanci
Bayanai sun nuna cewa Traore wanda laftanal ne a lokacin, ya nuna kwarewa wajen shugabanci, ciki har da "kasancewa mai kwazo da kasance na kusa da mutanensa."
Bayan aikin da ya yi a Mali, Traore ya bayar da gudunmuwa sosai wajen yaki da masu tayar da kayar baya a kasarsa ta Burkina Faso tsakanin shekarar 2019 zuwa 2022.
An yi masa karin girma zuwa mukamin kyaftin a shekarar 2020. Jim kadan bayan da ya kitsa juyin mulki da ya kifar da gwamnatin Damiba a watan Satumbar 2022, Traore ya ce shekararsa 34 — kuma batun ya sa wasu suna sanya shakku kan cancantarsa a matsayin shugaban kasa.
“Na san cewa ina da karancin shekaru idan aka kwatanta da dukkanku a nan. Ba mu so abin da ya faru ba (habarar da gwamnatin Damiba), amma ba mu da zabi ne," kamar yadda ya shaida wa jami'an gwamnati a watan Oktoban 2022.
Farin jininsa ya dan yi kasa a watan Yulin 2023, lokacin da ya jagoranci tawagar shugabannin kasashe 16 zuwa birnin Saint Petersburg a Rasha, inda suka gana da Shugaba Vladimir Putin, wanda ya shirya wani babban taron Rasha kan Afirka.
Wanda ya bambanta da saura
Takwarorinsa shugabannin kasashe suna sanya kwat mai tsada ne. Amma Traore wanda tsawonsa ya dara kafa shida, ya kan sanya kakin soja ne, da jar hula da kuma safar hannu.
Yayin da yake wucewa ta gaban jami'an tsaro wadanda suke sara wa shugabannin kasashen da suka isa wurin taron, Expo Forum, Traore yana cikin mutane kalilan, idan ma ba shi kadai ba, inda shi ma yake sara musu.
Idan wannan bai ja hankalin duniya ba, surar jikinsa da kuma yadda ya bambanta da saura za su ja — hatta a kusa da Putin — yayin da ya tsaya ya dauki hoto tare da jagoran Rasha.
Sarawar, a hotonsa da Putin da irin kayan da ya sanya su ne abubuwan da suka sa ya ja hankalin jama'a, amma jawabinsa yayin Babban Taron Rasha kan Afirka wanda aka yi tsakanin 27 zuwa 28 ga watan Yuli, ya sa an yaba masa.
"Matsalar ita ce shugabannin Afirka wadanda ba sa kawo wa mutanen da ke wahala komai, suna maimaita abin da Turawan mulkin mallaka suke fada mana. Saboda wannan sai su rika siffanta mu da wadanda ba sa kare hakkokin dan Adam," in ji Traore.
"Mu shugabannin kasashen Afirka, dole ne sai mun daina zama karnukan farautar Turawan mulkin mallaka."
‘Muna ciyar da mutanen kasarmu'
Ya kuma soki shugabannin Afirka wadanda "suke farin cikin karbar kyautuka."
"Jiya (27 ga watan Yuli), Shugaba Vladimir Putin ya sanar da (kyautar) hatsi da za a tura Afirka. Wannan abin farin ciki ne kuma muna godiya da wannan. Ko da yake wannan sako ne ga shugabanni a Afirka."
"Yayin taro na gaba, kafin mu zo nan sai mun tabbatar da wadatuwar abinci ga mutanenmu. Wajibi ne mu koyi haka daga wadanda suka yi nasara ta wannan fuska…," in ji Traore.
Kalamansa sun yi kama da wadanda Thomas Sandara ya yi a farkon shekarun 1980, wanda kamar Traore, shi ma ya hau karagar mulkin Burkina Faso ne ta hanyar juyin mulki.
'Sankara ya dawo'
A ranar 4 ga watan Oktoban shekarar 1984, Sankara, yayin wani taro na duniya — wato lokacin a Babban Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya — ya ce: "Burinmu ta fuskar tattalin arziki shi ne samar wa jama'ar Burkina Faso abinci sau biyu a rana da kuma ruwan sha."
A kafafen sada zumunta, mutane na cewa Sankara ne ya dawo. Ana tsakiyar bala'in yunwa a yankin Yammacin Afirka da ya shafi Burkina Faso da Mali da Chadi da kuma Nijar a farkon shekarun 1980, Sankara ya kifar da gwamnatin Faransa a Burkina Faso a ranar 4 ga watan Agustan shekarar 1983.
Juyin juya halin kishin Afirkan ya samu karbuwa a zukatan galibin 'yan Burkina Faso, inda ya gabatar da shirye-shiryen matakan yafe wa kasar basussuka da tsananin yunwa wadda ta jefa mutane cikin ukuba.
Yayin da matsalar yunwa ta kasance babban kalubale ga Burkina Faso a yau, matsalar tsaro ta fi ta zama babbar matsala.
Traore ya yi alkawarin yaki da masu tsattsauran ra'ayi kuma ya nemi goyon bayan sabbi kawayen kasar ciki har da Rasha.
Ya ce sojojinsa suna bukatar horo da kayan aiki da dabarun tattara bayanan sirri wadanda za su taimaka musu wajen yaki da masu tsautstsauran ra'ayi.
'Ya kasa nuna kwarewarsa a zahiri'
Yayin da ake ci gaba da yaba masa, wasu masu lura da al'amura sun ce har yanzu Traore bai yi wani muhimmin aiki ba ga mutanen Burkina Faso don samun cikakkiyar yardar su.
Wani mai sharhi kan al'amura dan Nijeriya Achike Chude ya ce ya kamata Traore ya "fitar da tsari a kasa" wanda zai ba shi damar yin manyan ayyuka.
"Zai dora ne a kan kalubalen da wanda ya gabace shi ya bari? Shugabanni da suka hau mulki ta hanyar juyin mulki ya kamata su cika alkawarin da suka dauka," kamar yadda Chude ya shaida wa TRT Afrika.
"Yana bukatar ya fitar da wani tsari a kasa, irin wanda lokacin da zai bar mulki, mutane za su iya kallonsa su ce: 'Gaskiya lokacin da sojojin suka yi mulki abubuwa ba su lalace ba sosai," in ji shi.
Haka zalika Chude ya soki matakan da Traore ya bi wajen darewa karagar mulki.
"Juyin mulki abu ne mai hadari sosai musamman idan ka yi kokarin hanbarar da gwamnatin soja. Mutane sun ce ya yi aikin kut da kut tare da Damiba, wanda ya gada. Wasu za su iya kallon hakan a matsayin cin amana," in ji Chude.
Ya ci gaba da cewa har yanzu ba a fahimci dalilin da ya sa Traore ya kifar da gwamnatin Damiba ba.
"Ba mu fahimci abin da ya sa ya yi haka ba. Tana iya yiwuwa ya yi hakan ne saboda son zuciya. Tana iya yiwuwa kuma ya yi hakan ne bisa kwakwkwaran dalili da kuma kishin kasa," in ji Chude.
Tarbar ban girma
Bayan tafiyarsa zuwa Rasha a watan Juli, 'yan Burkina Faso sun yi wa Kyaftin İbrahim Traore gagaruwar tarba, inda mutane da dama suka jeru a gefen titunan babban birnin kasar Ouagadougou.
Yaya aka yi ya fara samun manyan mukamai, kuma har ya zama shugaban kasa?
Traore ya fara karatu ne a wata makarantar sojoji bayan ya shiga aikin soja a shekarar 2009, lokacin yana da shekara 21 da haihuwa. Ya samu horon aikin soja ne a kasar Maroko.
Traore ya fara aikin soja gadan-gadan ne bayan kammala makarantar sakandare a birnin Bobo-Dioulasso City wanda yake kudu maso yammacin Burkina Faso. Rahotanni sun ce "ba ya magana sosai kuma yana jin kunyar jama'a", amma kuma "yana da hazaka."
Kafin hambarar da Damiba daga mulki, shi ne shugaban bangaren atilari a Burkina Faso.
Jim kadan bayan juyin mulkin watan Satumbar 2022, Traore ya ayyana kansa a matsayin jagoran Patriotic Movement for Conservation and Restoration, kuma kwana biyar bayan haka — a ranar 6 ga watan Oktoba – ya sanar cewa shi ne shugaban gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso.
Ya yi alkawarin mayar da mulki a hannu farar hula a Burkina Faso a watan Yulin shekarar 2024.