An kashe Idriss Deby a fagen daga bayan sake zabarsa a karo na shida /Photo AA

An soma mayar da martani kan hukucin daurin rai da rai da kotun kasar Chadi ta yanke wa ‘yan tawaye sama da 400 da aka same su da hannu a kisan tsohon shugaban kasar Idriss Deby.

An kashe Shugaba Deby ne a shekarar 2021 a fagen.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito lauyan da ke kare wadanda ake zargin Francis Djokoulde yana tabbatar da hukuncin da aka yanke na daurin rai da rai da kuma tara da za su biya kasar Chadi.

An soma shari’ar mambobin kungiyar ‘yan tawaye ta Libyan-based Front for Change and Concord in Chad (FACT) a ranar 13 ga watan Fabrairu a N’Djamena babban birnin kasar.

A ranar Talata 21 ga watan Maris ne sahen da ke shari’a kan laifuka na kotun daukaka kara na N’Djamena ya gano cewa mutum 441 da ake wa shari’ar suna da hannu a ta’addanci da zagon kasa ga tsaron kasa, da kuma barazana ga lafiyar shugaban kasar da sauran zarge-zarge.

Shugaban kungiyar ‘yan tawaye na FACT Mahamat Mahadi na daya daga cikin wadanda aka samu da laifin.

“Mun ji dadi kwarai ganin cewa mutanen da ke da hannu a mutuwar tsohon shugaban kasarmu an kama su da laifi, wannan hukunci ya yi, ” in ji Muhammad, wani mazaunin birnin N’Djamena.

Ya kuma kara da cewa "Mutane da dama a Chadi a halin yanzu sun samu sauki a zukatansu sakamakon radadin rasuwar shugabansu,

"Wannan shari’ar dauke take da darasi ga wadanda suke so su bi sahun irin wadannan ‘yan tawayen."

Alhaji Mustapha Ibrahim wanda shi ne Sarkin Hausawan Birnin N’Djamena ya shaida wa TRT Afrika cewa hukuncin kotun bai zo wa jama’a da mamaki ba ganin irin girman laifin da ake zarginsu da aikatawa .

Biyan diyya

A cewar Alhaji Ibrahim, diyyar da aka ce wadanda ake zargin su biya ba abu ba ce mai yiwuwa.

“Ba su da kudin da ake so su biya, sai dai idan wata kungiya ce za ta tallafa musu ta biya a madadinsu,” in ji Alhaji Ibrahim.

Kotun dai ta bukaci wadanda aka kama da laifin su biya sama da dala miliyan 30 ga kasar Chadi a matsayin diyya sannan sama da dala miliyan daya ga iyalan marigayi Debby.

Tausayi

Sai dai kamar yadda Adamu Muhammad ya bayyana, wasu jama’a musamman wadanda ke bangaren adawa na nuna tausayi ga wadanda aka kama da laifin inda suke cewa hukuncin da aka yanke musu ya yi tsauri.

“’Yan adawa na kallon wannan hukuncin a matsayin rashin adalci saboda ana zargin su ne kawai kuma hukuncin da aka yanke musu ya yi tsanani,” in ji shi.

An sanar da rasuwar Idriss Debby kwana guda bayan an sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar a 2021 domin mulkar kasar a karo na shida.

Bayan rasuwarsa, nan take dansa Mahamat Idriss Deby ya maye gurbinsa inda yake mulkar kasar a halin yanzu.

TRT Afrika