Jam'iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta bayyana cewa shugaban kasar Bola Tinubu ba ya bukatar kamun-kafa a shari'ar da ake kalubalantar nasararsa a zaben da ya gabata.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafin Twitter, APC ta ce zargin da wani Mista Jackson Ude ya yi cewa Shugaba Tinubu ya yi magana ta waya da Alkalin Alkalan kasar Mai Shari'a Olukayode Ariwoola kan batun ba gaskiya ba ne.
Hasalima jam'iyyar ta ce irin wannan zargi zai iya haddasa husuma.
A sanarwar da Sakataren Yada Labarai na jam'iyyar APC Felix Morka ya fitar, ya ce Mista Ude ya kirkiri karya ne kan wannan batu da ke da muhimmanci ga kasar wanda ke gaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa.
Ya ce shakka babu Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC sun lashe zaben shugaban kasar ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 kuma ba ya bukatar kamun-kafa wajen Alkalin Alkalan kasar dangane da karar.
Sakataren jam'iyyar ya ce 'yan Nijeriya suna da basira kuma za su yi watsi da wadannan kalamai marasa tushe na 'yan adawa da sojojin haya.
Atiku Abubakar da Peter Obi ne 'yan takarar da suka zo na biyu da na uku a zaben kuma sun garzaya kotu domin kalubalantar zaben da aka yi wanda Tinubu ya samu kashi 37 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar.