A watan oktoban 2018 ne Jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo da ake zargin Ganduje ne a ciki ana mika masa kudi yana karba. Hoto: OTHERS

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa ta Jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nijeriya, ta ce ta aika wa tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje gayyata zuwa ofishinta.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Alhamis, ta ce ta gayyaci Dokta Ganduje ne don jin bahasi a kan wani bidiyon da aka taba saki inda ake zargin gwamnan "yana karbar daloli tare da saka wa a cikin aljihunsa."

"Biyo bayan alwashin da ya sha na bin doka da oda kan binciken da ake yi kan bidiyoyin da ake zargin tsohon gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na karbar daloli, shugaban hukumar ta PCACC Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya ce hukumar ta aika wa tsohon gwamnan sammaci don ya bayyana a gabanta," in ji sanarwar.

Barista Rimin Gado ya fara sanar da batun gayyatar gwamnan ne a yayin da ake wata tattaunawa da shi a wani shiri na gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, inda ya ce hukumar na sa ran Ganduje ya bayyana a gabanta a mako mai zuwa don samun damar gyara sunansa a kan binciken da ake yi.

Sanarwar ta ce yayin da aka tambayi Rimin Gado kan ko hukumar tasa za ta ci gaba da binciken da take yi , sai ya ce "Na sanya hannu kan wasikar gayyatarsa don ya zo ya amsa wasu tambayoyi a mako mai zuwa, saboda haka doka ta ce kuma za mu ba shi isasshiyar dama don kare kansa."

Sannan da aka sake tambayarsa kan ko me hukumar za ta yi idan har tsohon gwamnan bai amsa gayyatar ba, sai ya ce "Akwai tanadin da doka ta yi, shari'a tana da karfi kuma takan sa a yi biyayya.

"Shari''a ba za ta ba ka damar yin kamun-kafa ba. Akwai matakai kuma za mu bi dukkan matakan da suka dace don yin abin da ya kamata," in ji Rimin Gado.

A watan oktoban 2018 ne Jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani bidiyo da ake zargin Ganduje ne a ciki ana mika masa kudi yana karba.

Bidiyon ya jawo cece-ku-ce sosai ba a Jihar Kano ba kawai har ma a Nijeriya baki daya. Sai dai a hirar da aka sha yi da tsohon gwamnan ya sha musantawa yana cewa bidiyon ba gaskiya ba ne, hada shi aka yi, inda har ya sha alwashin daukar mataki kan lamarin.

TRT Afrika