Hukumar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ƙaryata wani labari da ake ta yaɗawa a shafukan sada zumunta da ake zarginta da bai wa mahajjata abinci ɗan kaɗan.
A ranar Talata ne aka fara yaɗa hoton nau’in abincin karin kumallo da ke nuna kunu kaɗan a wani mazubi da kuma ƙosai ƙwaya uku, inda aka ce wani ɗan jarida ne ya fara yaɗawa don nuna wa duniya yadda ake “bai wa mahajjata abinci kaɗan bayan biyan naira miliyan takwas kuɗin kujerar ajji.”
Lamarin ya jawo Allah wadai a shafukan intanet a Nijeriya, inda aka dinga zargin hukumar da “son wulaƙanta alahazai” kan irin nau’in abincin da take ba su duk da makuɗan kuɗaɗen da suka biya.
Sai dai a sanarwar da ta fitar a ranar Talata da marece mai ɗauke da sa hannun Hajiya Fatima Sanda Usara, mai magana da yawun NAHCON, ta ce “an jawo hankalinmu kan wani labarin ƙarya da shafin Facebook na wani Babagana Digima ya wallafa, da ke nuna wani nau’in abinci da aka ce shi muke raba wa alhazan Nijeriya bayan da suka biya kuɗin kuerar Hajji har naira miliyan takwas.”
“Bayan yin abin da ya dace a kan labarin daga tushe mun yi imani cewa dokokin watsa labarai ba su yarda ɗan jarida da ya san abin da yake yi ya dogara da labari daga Facebook kaɗai ba. Wani abin takaici shi ne cewa ɗan jaridar da ya ɗauki labarin daga Facebook yana nan a Nijeriya bai je Saudiyyan ba,” in ji sanarwar.
NAHCON ta ce da samun labarin ba ta yi ƙasa a gwiwa ba sai ta ja hankalin wanda ya fara ƙirƙirarsa a fili da a bayyane kan rashin sahihancin ikirarin nasa inda ta nemi ya janye zargin, tana mai yi masa uzurin ko bisa rashin sani ya wallafa, amma sai ya ƙi yin hakan.
“Duk da haka alhazai da dama da suke Makkah a halin yanzu sun yi ta ƙaryata zargin nasa ta hanyar wallafa hotunan ainihin abincin da ake ba su a ƙasan labarin da ya wallafa, sannan ma’aikatan NAHCON ma da suke can sun yi bayanin irin abincin da ake bayarwa, suna masu cewa hoton da ya saka din an yi masa kwaskwarima ne, kuma ƙarya ce tsagwaronta.
“Amma duk da haka gidan jaridar Sahara Reporters sun yi biris da hakan. Kuma jaridar ta yi amfani ne kawai da wani hoto na mahajjatan Babban Birnin Tarayya na abin karyawar da aka ba su a otel dinsu a Makkah, amma sai aka yi masa kwaskwarima aka wallafa shi.
A ƙarshe hukumar Alhazan ta yi kira ga al’umma da su yi watsi da labarin ƙaryar da ake watsawa a kan batun abin karyawar tana mai nanata cewa ƙarya ce da son ɓata mata suna.