Gwamnatin Nijeriya ta gudanar da jana'izar ban-girma ga sojoji 17 da wasu ɓata-gari suka kashe a ƙauyen Okuama na Jihar Delta lokacin da suka je kwantar da tarzoma a rikicin ƙabilanci da ke faruwa a yankin.
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ne ya jagoranci jana'izar ranar Laraba a Maƙabartar Soji ta Ƙasa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.
Shugaba Tinubu ya jaddada ta'aziyyarsa ga iyalan sojojin, yana mai jinjina wa dakarun bisa irin sadaukarwar da suka yi domin wanzar da zaman lafiya a Nijeriya.
"Gwamnatin tarayya za ta ɗauki nauyin karatun ƴaƴan dukkan sojojin Nijeriya da aka kashe a Okuama na Jihar Delta har zuwa matakin jami'a, ciki har da waɗanda ake da cikinsu," in ji wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar.
Kazalika Shugaba Tinubu ya umarci hukumomi su tabbatar sun biya iyalan sojojin dukkan kuɗaɗen da suka kamata a ba su cikin kwana 90.
Haka kuma shugaban ƙasar ya ce gwamnatin tarayya za ta bayar da gida ga iyalan kowane soja da aka kashe a ko ina suke so a faɗin Nijeriya.
An karrama manyan sojojin da lambar yabo ta Members of the Order of Nigeria (MON), yayin da aka bai wa ƙanana daga cikinsu lambar yabo ta Officers of the Federal Republic.
A yayin da yake jawabi, shugaban rundunar tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya sha alwashin zaƙulo waɗanda suka kashe sojojin, yana mai cewa babu wata farfaganda da za ta hana su hukunta mutanen da suka yi wannan ɗanyen-aiki.