A Maris na 2020, sojojin Chadi sun samu mafi munin asarar rayuka a yankin lokacin da dakarunta 100 suka mutu a wani hari kan yankin tafkin Bohoma. / Hoto: Reuters

Gwamnatin Chadi ta ce wani mummunan harin ƙungiyar Boko Haram kan sojojin ƙasarta ya halaka kusan mutum 40 cikin daren Lahadi, a kusa da iyakarta da Nijeriya.

Majiyoyin gwamnatin Chadi da kuma na yanki sun faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Litinin cewa, "'Yan Boko Haram sun kai hari kan wani sansanin sojoji da ke ɗauke da soja sama da 200" a daren Lahadi.

Fadar Shugaban Ƙasa ta faɗa a wata sanarwa cewa harin ya faru kusa da Ngouboua a yammacin ƙasar, kuma "mummunan harin ya halaka kusan mutane 40".

Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno ya ziyarci wajen da abin ya faru ranar Litinin kuma ya ƙaddamar da wani shiri "don farautar maharan da nemo su a maɓoyarsu".

Sanarwar ta ce harin ya faru ne da ƙarfe 10:00 na dare agogon yankin (2100 GMT), cewar majiyar a zantawa da AFP.

"'Yan Boko Haram sun karɓe iko da sansanin, sun ƙwace makamai, sun ƙona moroci da ke da makamai, sannan suka gudu," cewar wani mazaunin yanki wanda ya ce kar a ambaci sunansa.

Yankin Tafkin Chadi yana da yankuna kogi da fadama yana zama maɓoyar 'yan ƙungiyoyin jihadi kamar Boko Haram da ire-irensu Islamic State in West Africa (ISWAP), wanda ke kai hare-hare kan sojojin ƙasashe da farar-hula.

Boko Haram dai ta ƙaddamar da yaƙin ta'addanci kan Nijeriya a 2009, wanda ya haifar da mutuwar mutane 40,000 da ɗaiɗaita mutane miliyan biyu, kuma ƙungiyar ta fantsama zuwa ƙasashe maƙota.

A Maris na 2020, sojojin Chadi sun samu mafi munin asarar rayuka a yankin lokacin da dakarunta 100 suka mutu a wani hari kan yankin tafkin Bohoma.

Harin ya janyo shugaban ƙasar a lokacin, Idriss Deby Itno mahaifin shugaban yanzu, ya kaddamar da yaƙi kan 'yan jihadi.

A watan Yuni, ƙungiyar kula da 'yan gudun hijira ta International Office for Migration (IOM) ta ce mutane 220,000 aka taggayara a hare-haren ƙungiyoyi ta'adda a yankin Tafkin Chadi.

AFP