Kawo yanzu an kashe fiye da mutum 10,000 tun da rikicin ya barke a Sudan, a cewar kungiyar the Armed Conflict Location & Event Data project da ke bin diddigin rikicin. / Hoto: AFP

Fiye da mutum 20 ne suka mutu ranar Lahadi bayan wani hari da aka kai ta sama ya sauka fada kan wata kasuwa a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, a cewar wata kungiyar lauyoyi da ke goyon bayan kafa mulkin dimokuradiyya.

Wannan shi ne hari na baya-bayan nan tun bayan barkewar yaki a watan Afrilu tsakanin dakarun sojin kasar da ke karkashin jagoran soji Janar Abdel Fattah al-Burhan da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke shugabantar rundunar Rapid Support Forces (RSF).

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce makaman da aka harba ta sama sakamakon gumurzun da ake yi tsakanin bangarorin biyu sun sauka a kasuwar birnin Omdurman.

"An kashe fararen-hula sama da 20 sannan aka jikkata wasu da dama," in ji sanarwar wadda aka aika wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Kungiyar tana bibiyar irin cin zarafin da ake yi wa fararen-hula a yakin da ake gwabzawa tsakanin Janar-janar na soji biyu.

Ranar Asabar, wata majiya daga fannin kiwon lafiya ta ce harin da aka kai ta sama ya fada kan gidaje a Khartoum inda ya kashe fararen-hula 15.

Omdurman ya kasance wani yanki da yake yawaita yin ba-ta-kashi tsakanin bangarorin da ke yaki da juna a Sudan.

Ko da yake an magance galibin hare-haren da a baya ake kaiwa a babban birnin kasar da kuma yankin Darfur da ke yammaci, sai dai rikicin ya watsu zuwa kudancin Khartoum a cewar ganau.

Kawo yanzu an kashe fiye da mutum 10,000 tun da rikicin ya barke a Sudan, a cewar kungiyar the Armed Conflict Location & Event Data project da ke bin diddigin rikicin.

TRT Afrika da abokan hulda