Ministan Kuɗi na Nijeriya Wale Edun ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa an ƙara harajin kayayyaki daga kaso 7.5 cikin 100 zuwa kaso 10.
Ministan ya bayyana haka ne a wata sanarwar da ya saka wa hannu wadda ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar na zuwa ne bayan jita-jitar da aka rinƙa yaɗawa kan cewa an ƙara haraji, lamarin da ya jawo tuni wasu daga cikin sanannun ‘yan Nijeriya ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar suka soma ƙorafi.
“Harajin VAT a halin yanzu kaso 7.5 ne kuma shi ne abin da gwamnati ke amsa a kan kayayyaki waɗanda ke da haraji a kansu. “Don haka gwamnatin tarayya ko wata hukuma ba za su iya ɗaukar wani mataki da ya saɓa wa abin da dokar mu ta nuna ba,” in ji ministan.
“Tsarin haraji yana tafiya ne kan ginshiƙai uku, waɗanda suka haɗa da manufofin haraji da dokokin haraji da gudanarwar haraji. Akwai buƙatar duka ukun su samar da yanayi mai kyau da zai tattara kuɗin shiga na gwamnati.
“Abin da muke mayar da hankali a matsayinmu na gwamnati shi ne amfani da tsare-tsaren haraji da tasarrufin kuɗaɗe ta hanyar da za a ƙara haɓaka tattalin arziƙi da rage talauci da bunƙasa harkokin kasuwanci,” kamar yadda ministan ya ƙara da cewa.
Duka waɗannan batutuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriyar ke ƙorafi kan ƙarin kuɗin man fetur da aka yi a ƙasar, wanda tuni farashin kayayyaki a kasuwa ya soma ƙaruwa.