Gwamnatin jihar Yobe a arewa maso gabashin Nijeriya ta nesanta kanta daga zargin cewa ta hada baki da sojojin kasar wajen zubar da cikin mata ‘yan gudun hijira 10,000.
Wata sanarwa da hukumar kare hakkin bil Adama ta Nijeriya ta fitar a ranar Litinin, ta ambato babban kwamishina shari'ar jihar Yobe, Mista Saleh Samanja, yana cewa karon farko kenan da yake jin labarin.
A kwanakin baya ne kamfanin dillacin labaran Reuters ya fitar rahoto yana zargin cewa gwamnatin Jihar Yobe ta hada baki da sojoji wajen zubar wa ‘yan gudun hijira 10,000 ciki tare da kashe yara da kuma cin zarafin mata.
Sai dai da ya bayyana a gaban kwamitin bincike na hukumar kare hakkin bil Adama ta Nijeriya a karkashin jagorancin mai shari’a Abdu Aboki, kwamishinan shari’ar Jihar Yobe ya ce labarin ma ya ci karo da hankali don babu wata gwamnatin da za ta yarda a kashe mutane haka kawai.
Sanarwar ta ce kwamishinan shari'ar jihar ya ce shi da kansa ya kafa cibiyar jin karar cin zarafi a jihar, inda ya ce cibiyar ta saurari kararraki da suka hada da na fyade da sauransu.
Ya ce a matsayinsa na shugaban cibiyar, ya kamata ya san da irin wannan abu idan ya faru.
Tun da fari kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce ya yi rahoton nasa ne bayan da ya yi hira da mata da 'yan mata 33.
Kawo yanzu Reuters bai ce komai game da maganar da gwamnatin jihar Yoben ta yi ba.