Gwamnatin Nijar ta amince a gina sabbin filayen jiragen sama

Gwamnatin Nijar ta amince a gina sabbin filayen jiragen sama

Mahukuntan ƙasar na son haɓaka harkokin mai da masana'antu da makamashi.
Kazalika majalisar ministocin ta amince da dokar rusa wani ɓangare na gandun dabbobin Dosso da ya kai kadada 7,877 domin gina matatar mai. . Photo: Presidence du Niger/ X

Majalisar ministocin Nijar ranar Alhamis ta amince da dokar kafa ƙananan filayen jiragen sama huɗu a kusa da kan iyakar ƙasar da ƙasar Benin.

Majalisar ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Abdourahmane Tiani ta amince da dokar ne bayan kamfanin bututun mai na Yammacin Afirka (WAPCO) ya nemi a ba shi damar gina filayen jiragen masu zaman kansu domin sintirin ma’aikata a tashoshin tura mai ta bututan man da ke tsakanin Nijar da ƙasar Benin.

Kazalika majalisar ta amince da dokar rusa wani ɓangare na gandun dabbobin Dosso da ya kai kadada 7,877 domin gina matatar mai.

Ana ganin ci-gaban fannin mai da haƙar ma’adinai da makamashi da kuma masana’antu da hukumomin Nijar ke son samarwa a yankin Dosso zai samar da aikin yi tare da ƙara wa gwamnati kuɗin-shiga.

TRT Afrika