An ta yi zanga-zanga a Kenya bayan cire tallafin fetur. Hoto/

Kasar Kenya ta mayar da tallafin man da ta cire watanni 11 da suka gabata. Shugaba William Ruto ne ya cire tallafin a baya inda a lokacin ya ce ba abu ne mai dorewa ba.

Tattalin arzikin kasar, mafi girma a Gabashin Afirka na fama da hauhawar farashin kayayyakin abinci da man fetur, kuma cire tallafin fetur din na zuwa ne bayan karin haraji da aka yi.

A wata sanarwa, hukumar da ke kula da makamashi ta kasar ta ce za a yi amfani da kudin tallafin domin biyan diyya ga kamfanonin mai. Wannan na nufin farashin fetur ba zai sauya ba har zuwa wata mai zuwa a lokacin da za a sake yin bitar farashin.

Rage radadin talauci

“Gwamnatin Kenya ta kudiri aniyar daidaita farashin man fetur na Agusta-Satumba domin rage radadin hauhawar man fetur ga kwastamomi sakamakon karin kudin fetur da karuwar kudin gidaje,” a cewar hukumar makamashi da man fetur ta kasar.

A watan jiya gwamnatin Kenya ta rubanya harajin da ke kan man fetur zuwa kashi 16 cikin 100 a wata doka wadda ta kuma fito da wani tsari kan kashi 1.5 na gida ga duka ma’aikata da kuma kara haraji kan harajin yau da kullum zuwa kashi 35.

A halin yanzu dai wannan sabuwar dokar na gaban kotu inda ake kalubalantarta.

TRT Afrika