Gwamnatin Kaduna ta gargaɗi ƴan jarida kan su rinƙa tantance labarai kafin yaɗawa. / Hoto: Uba Sani

Gwamnatin Jihar Kaduna ta musanta wani rahoto da ke cewa ta ɗauki hayar wani mai shiga tsakani domin taimaka mata wurin ceto ɗalibai kusan 300 da aka sace a jihar.

A wata sanarwa da gwamnatin ta Kaduna ta fitar a ranar Asabar, ta nesanta kanta da labarin wanda jaridar Punch a ƙasar ta wallafa a ranar 9 ga watan Maris.

“An ja hankalin gwamnatin Kaduna kan wani labari ƙarya da jaridar Punch ta wallafa a ranar 9 ga watan Maris ɗin 2024 inda ta ce Gwamnatin Kaduna ta yi hayar wani mai shiga tsakani na musamman domin taimakawa wurin dawo da ɗaliban makarantar da aka sace a Kuriga, da ke Ƙaramar Hukumar Chikun.

“Muna so mu tabbatar da cewa Gwamnatin Kaduna ba ta ɗauki hayar wani mai shiga tsakani ba, kuma ba mu tunanin ɗaukar wannan matakin,” kamar yadda gwamnatin ta bayyana a sanarwar da ta fitar.

Gwamnatin jihar ta ce tana da tsare-tsare na musamman waɗanda suka shafi tattaunawa da ƴan ta’adda da masu aikata laifuka.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne ƴan bindiga suka kai hari ƙauyen Kuriga a Ƙaramar Hukumar Chikun da ke Jihar Kaduna inda suka sace kusan ɗalibai 300.

Tun bayan sace ɗaliban, gwamnan jihar Malam Uba Sani ya kai ziyara ƙauyen na Kuriga inda ya tabbatar da cewa za su yi iyakar bakin ƙoƙarinsu domin ceto waɗannan ɗaliban.

Haka kuma bayan sace waɗannan ɗaliban da kwana guda wasu ƴan bindigan suka kai kai hari kan ɗaruruwan Musulmai a yayin da suke sallar Juma'a a wani yanki na Birnin Gwari da ke jihar Kaduna

TRT Afrika