Gwamnatin Kaduna da ke arewacin Nijeriya ta dauki matasa dubu bakwai domin gudanar da aikin sa-kai na bijilanti a jihar.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki matasan ne domin tallafa wa jami’an tsaron gwamnatin tarayya a ayyukan da suke yi na samar da tsaro.
Yayin da ake kaddamar da soma horar da sabbin ‘yan bijilantin ranar Lahadi, Gwamnan Jihar Uba Sani ya bayyana cewa zai yi iya bakin kokarinsa domin magance matsalolin da suka shafi fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma sauran abubuwan da ke yi wa al’ummar Jihar Kaduna barazana.
Daga cikin sabbin ‘yan bijilantin da aka dauka, akwai mata da maza wadanda suka fito daga kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna.
Gwamnan ya bayyana cewa za a kai ‘yan bijilantin zuwa kauyuka domin taimaka wa jami’an tsaro.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Nijeriya da ke fama da matsalolin tsaro wadanda suka hada da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Ko a watan Yuni sai da rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta tabbatar da kama mutum 503 da take zarginsu da aikata miyagun laifuka da suka hada da fashi da satar dabbobi da satar mutane da kisan kai da kwacen wayoyi da sauran laifuka.
Haka kuma a cikin makon nan sai da ‘yan bindiga suka hari ga wasu masu ibada a jihar inda suka kashe akalla mutum hudu.