Wannan ne karo na uku da Sheikh Daurawa ke zama shugaban Hisbah/ Hoto: Sheikh Daurawa Facebook

Gwamnan Jihar Kano a arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya nada fitaccen malamin Islaman nan Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin Kwamandan Rundunar Hisbah na jihar.

A wani bidiyo da ya aka wallafa a wani shafin mabiya Kwankwasiyya a Twitter, an ga sakataren gwamnatin jihar Dokta Baffa Bichi yana mika wa Sheikh Daurawa takardar nadin, a ranar Litinin.

"Akaramakalla a madadin Mai Girma Gwmanan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ina mika maka wannan takardar kama aiki a matsayin babban kwamanda janar na hukumar Hisbah ta jihar Kano.

"Allah Ya yi jagoranci, Allah Ya ci gaba da taimakonmu, Allah Ya sa a yi nasara a gudanar da ayyuka na alheri domin ci gaban al'umma. Allah Ya ba mu sa'a," in ji Dokta Bichi a yayin da yake mika wa Daurawa takardar tare da yin musabiha da shi.

A nasa bangaren, bayan da ya karbi takardar nadinsa nasa, babban malamin ya yi adduar cewa "Allah Ya sa albarka, Allah Ya taimake ka Ya taimaki Mai Girma Gwamna, Allah Ya ba mu ikon sauke nauyin da aka dora mana.

"Allah Ya kara bunkasa Jihar Kano. Allah Ya taimaki gwmana Ya ba shi nasara. Allah Ya sa mu gama lafiya," inda sauran mutanen da ke wajen suka amsa da "Ameen, ameen."

Wannan dai shi ne karo na uku da Sheikh Daurawa ke samun mukamin shugabancin hukumar Hisbah.

Wane ne Sheikh Aminu Daurawa?

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa haifafen Unguwar Kofar Mazugal ta karamar hukumar Dala ne a Jihar Kano. An haife shi ranar 1 ga watan Janairun 1969.

Malamin ya soma karatun Kur'ani tun yana karami, sannan ya yi haddarsa yana da shekara 15, kamar yadda wani makusancinsa ya shaida mana.

Sheikh Daurawa ya fara da karatun firamare amma bai ci gaba da sakandare ba sai da ya haddace Kur'ani, bisa tsarin gidansu.

Sheikh Daurawa ya kuma ci gaba da neman ilimin addini bayan kammala firamare da sakandare, a wajen manyan malamai daban-daban a Jihar Kano.

Ya yi karatun difiloma a fannin sarrafa bayanan komfuta.

Sannan ya fara karatun aikin jarida a Jami'ar Bayero ta Kano amma wasu dalilai suka hana shi karasawa.

A baya ya taba rike mukamin Kwamandan Hisba tsawon shekara takwas kafin daga baya a sauke shi a lokacin gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

TRT Afrika