Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya sauke wani Kwamishinansa da ya yi barazana ga alkalan da ke sauraron shari'ar gwamnan jihar.
A wani bidiyo da aka rika yadawa a shafukan sada zumunta, an jiyo Kwamishinan Kasa da Tsare-Tsare, Adamu Kibiya yana neman alkalan kotun su zaba tsakanin rayuwarsu ko aikinsu idan suka yanke hukuncin da "bai dace ba."
Gwamna Abba Kabir ya sanar da wannan mataki ne a wajen wani taron manema labarai na gaggawa da ya kira a fadar gwamnatin Kano a ranar Juma'a da daddare.
“Mutane sun zabe mu kuma wasu suna kokarin yin rashin adalci. Muna son shaida wa alkalan nan cewa ba za mu lamunci hakan ba. Duk wani alkali da yake da aniyar kwace mana 'yancinmu to zai yi da-na-sanin hakan.
"Duk abin da zai faru, babu ruwanmu...," kwamishinan ya fada a wani taro na 'yan jam'iyyar NNPP da aka yi a jihar.
A sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran jihar Baba Halilu Dantiye ya fitar bayan taron, gwamnatin Kano ta nesanta kanta daga kalaman Kwamishina Kibiya.
Wani labarin mai alaka: 'Muna rokon Allah ya bai wa Abba Gida-Gida hikimar warware matsalar da aka shuka a Kano'
Kalaman rashin da'a ga mataimakin shugaban kasa
Kazalika gwamnan jihar ya kuma sauke Mai ba shi Shawara na Musamman kan Matasa da Wasanni Yusuf Imam kan kalaman rashin da’a da ya ce ya yi kan mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima.
“A yayin da muke Allah wadai da barazanar da aka yi wa alkalai da kuma rashin da’ar da aka yi wa mataimakin shugaban kasa, muna so mu bayyana karara cewa wadancan kalamai ba sa wakiltar matsayin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf,” in ji sanarwar.
Yana da muhimmanci a fahimci cewa dukkan wadannan jami’an biyu babu wanda ya samu izini daga gwamnati cewa zai yi magana a madadinta, kuma babu mai magana da yawun gwamnati a cikinsu, sanarwar ta kara da cewa.
Gwamnatin Jihar Kano karkashin Abba Kabir tana matukar daukar bangaren shari’a da muhimmanci tare da bai wa alkalan da jami’an kotu girmansu da daraja su.
"Sannan a fahimtar da ke tsakanin gwamnatin Jihar Kano da al'ummarta da kuma Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamna Abba Kabir Yusuf yana matukar girmama Kashim Shettima kuma ba zai lamunci duk wani abu na rashin ladabi gare shi ko duk wani shugaba na Nijeriya ba," ya ce.
Sannan a karshe gwamnatin ta ba da umarnin cewa daga yanzu babu wani jami’in gwamnati da zai yi magana a kan duk wata matsala da ba ta shafi ma’aikatarsa ba idan har ba a ba shi izini ba.