Mahukunta a ƙasar Guinea sun rusa jam'iyyun siyasa da dama tare da sanya ido kan wasu manyan jam'iyyun adawa biyu a ranar Litinin.
Ƙasar wadda ke Yammacin Afirka tana ƙarkashin mulkin soji ne tun bayan hamɓarar da shugaba Alpha Conde da aka yi shekarar 2021.
Ƙungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta matsa ƙaimi wajen ganin an dawo da mulkin farar-hula, tare da gudanar da zaɓe a shekarar 2025, sai dai kawo yanzu gwamnatin rikon-ƙwarya ta ƙasar ba ta sanar da lokacin gudanar da zaɓe ba.
Ba a taɓa ɗaukar irin wannan mataki na rusa jam'iyyun siyasa har guda 53 a tarihin ƙasar Guinea ba wadda ta gudanar da zaɓenta na farko a tsarin dimokuraɗiyya a shekarar 2010 bayan shafe shekaru da dama ana mulkin kama-karya.
Ma'aikatar kula da ayyukan yankunan ƙasar ta bayyana wannan sanarwar ce bayan tantance dukkan jam'iyyun siyasar ƙasar da aka soma a watan Yuni.
A cewar ma'aikatar an ɗauki matakin ne domin ''tsaftace harkokin siyasa'' na ƙasar.
Jam'iyyar tsohon shugaban ƙasa
Jam'iyyu 67 da za a sa ido a kan su har na tsawon watanni uku za su ci gaba da yin aiki kamar yadda aka saba amma dole ne su kawar da matsalolin da aka samu a cikin rahoton da aka fitar.
Daga cikin jam'iyyun har da Rally of the Guinean People, jam'iyyar tsohon shugaban ƙasar Alpha Condé, da wata babbar jam'iyyar adawa, Union of Democratic Forces of Guinea.
Hukumomin ƙasar sun ce jam’iyyun da aka sanya ƙarƙashin sa ido sun gaza gudanar da taron jam’iyyarsu a cikin wa’adin da aka ƙayyade tare da ba da bayanan bankinsu da dai sauransu.
Guinea na daya daga cikin ƙasashen Yammacin Afrika masu tasowa ta fuskar ci gaba ciki har Mali, da Nijar da kuma Burkina Faso, waɗanda dukka sojoji suka karɓe mulki tare da jinkirta dawo da mulkin farar-hula.
A farkon wannan shekara ne gwamnatin mulkin soja a Burkina Faso ta tsawaita wa'adin miƙa mulki ga farar-hula da shekaru biyar.
Saɓa alƙawari
Kanar Mamadi Doumbouya wanda ke jagorantar mulkin Guinea, ya yiwa shugaban ƙasar juyin mulki shekaru uku da suka wuce, bayan da ce ya yi ƙoƙarin hana ƙasar faɗawa cikin ruɗani ne tare da ladabtar da gwamnatin da ta shuɗe kan saɓa alƙawari.
Sai dai tun bayan hawansa kan mulki wasu ke sukar sa da cewa bai fi wanda ya gaba daga mulki da komai ba.
A watan Fabrairu, shugaban mulki na sojin ya rusa gwamnatin ba tare da wasu ƙwararan bayanai ba, yana mai cewa za a naɗa wata sabuwa.
Doumbouya ya yi fatali da yunkurin da ƙasashen Yamma da sauran ƙasashe da suka ci gaba ke yi na shiga tsakani a siyasar Afirka da ke fama da kalubale, inda ya ce 'yan Afirka sun gaji da yadda kowa ke ƙoƙarin tsoma baki da abubuwan da suka shafe yankin.''