Gobarar da ta tashi a ɗakunan kwanan ɗalibai a wata makarantar firamare a Kenya ta kashe ɗalibai 17 tare da jikkata 13, kamar yadda rundunar 'yan sandan ƙasar ta bayyana ranar Juma'a.
Wasu daga cikin ɗaliban sun ƙone sosai har ba a iya gane su, a cewar ganau. Ana fargaba adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru, in ji 'yan sanda.
"Na bayar da umarni ga hukumomi su gudanar da cikakken bincike game da wannan mummunan lamari. Za a hukunta duk wanda aka samu da hannu a kan wannan batu," a cewar shugaban ƙasar Kenya William Ruto a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X.
Ƙungiyar bayar da agaji ta Kenya Red Cross ta wallafa saƙo a shafin X da ke cewa tuni hukumomi suka rufe makarantar.
An soma gudanar da bincika game da gobarar da ta tashi a makarantar firamare ta Hillside Endarasha da ke yankin Nyeri, a cewar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Kenya Resila Onyango.
Ana yawan samun tashin gobara
“Muna gudanar da bincike kan abin da ya haddasa gobarar kuma za mu ɗauki matakin da ya dace,” in ji shi.
A shekarun baya bayan nan, ana yawan samun tashin gobara a Kenya, da yawa daga cikinsu ana tashinsu ne da gangan.
Ɗalibai aƙalla 10 suka mutu a gobarar da ta tashi a wata makaranta a Nairobi a watan Satumba na 2017, wadda gwamnati ta ce da gangan aka tashe ta.
Aa shekarar 2001, ɗalibai 58 sun mutu sakamakon gobarar da ta tashi da ɗakunan kwanansu a makarantar Sakandare ta Kyanguli da ke wajen birnin Nairobi. Kazalika a shekarar 2012, ɗalibai sun mutu a makarantar Homa Bay County da ke yammacin Kenya.