Gwamnatocin kasashen Ghana da Afirka ta Kudu sun amince 'yan kasashensu da ke dauke da fasfo na gama-gari su shiga kasasshen juna ba tare da biza ba.
Daga ranar 1 ga watan Nuwamban 2023, 'yan Afirka ta Kudu da takwarorinsu na Ghana da ke rike da fasfo na gama-gari za su iya shiga kasashen juna ba tare da biza ba, a cewar wata sanarwa da ma'aikatun harkokin wajen kasashen suka fitar ranar Juma'a.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta fitar ta kara da cewa 'yan kasashen biyu za su iya shiga Afirka ta Kudu ko Ghana su kwashe tsawon kwana 90 ba tare da yin wani aiki ba.
"Ma'aikatar harkokin waje da hadin kan Ghana tana sanar da jama'a cewa Jamhuriyar Ghana da Jamhuriyar Afirka ta Kudu sun amince da yarjejeniyar dage neman biza ga masu rike da fasfo na gama-gari.
"Matafiya suna iya ya da zango, ko su fita ko kuma su zauna a kasashen biyu tsawon kwana 90 ba tare da sun yi aiki ba," in ji sanarwar.
A nasu bangaren, wata sanarwa da ofishin jakadancin Afirka ta Kudu da ke Ghana ya fitar ta ce ana sa rai bayan kwana 90 masu rike da fasfo din kasashen za su nemi biza.
Masana na kallon wannan mataki a matsayin wanda zai yaukaka dangantakar cinikiyya da sauran harkoki tsakanin kasashen biyu.