Ma'aikatar Harkokin Cikin gida ta Jamhuriyar Nijar ta ce ta umarci sassan bincike na ƙasar da su kasance cikin shirin ko ta kwana bayan da fursunoni suka tsere a ranar Alhamis daga gidan yari mai cike da mai tsaro na Koutoukale inda ake tsare fursunonin da suka haɗa da masu ikirarin jihadi.
Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ba ta bayyana adadin fursunonin da suka tsere daga Koutoukale da ke da tazarar kilomita 50 daga arewa maso yammacin Yamai babban birnin kasar ba, ko kuma yadda suka yi hakan. A cikin shekarun 2016 da 2019, an taɓa daƙile yunƙurin fasa gidan yarin.
Fursunonin gidan yarin sun hada da wadanda ake tsare da su daga rikicin kasar da kungiyoyin da ke ɗauke da makamai masu alaƙa da al Qaeda da IS da kuma wadanda ake zargin mayakan Boko Haram ne.
Hukumomin yankin sun kafa dokar hana fita da dare a cikin garin Tillaberi, wanda ke yanki daya da gidan yarin, amma ba su yi ƙarin bayani ba.
Jamhuriyar Nijar da maƙwabtanta da ke tsakiyar yankin Sahel na cikin sahun gaba wajen yaƙi da masu ikirarin jihadi da ke ci gaba da ƙaruwa tun shekarar 2012, lokacin da mayaƙan da ke da alaƙa da al-Qaida suka fara ƙwace wasu sassan kasar ta Mali.
Thousands have been killed in the insurgencies and more than 3 million displaced, fuelling a deep humanitarian crisis in some of the w orld's poorest countries.
Dubban mutane ne aka kashe a cikin tashe-tashen hankulan tare da raba wasu sama da miliyan uku da muhallansu, lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin jinƙai a wasu ƙasashe mafiya talauci a duniya.