A watan Janairun bana kawai sai da aka ceto ‘yan ci-rani kusan 90 daga kasashen Senegal, Gambia, Guinea-Bissau da Saliyo a gabar tekun Cape Verde. Hoto:

Fiye da mutum 60 ne aka yi amannar sun rasa rayukansu bayan da aka gano wani jirgi dauke da ‘yan ci-rani da ya tashi daga Senegal a kusa da gabar teku na tsibirin Cape Verde, a cewar Hukumar Kaura ta Kasa da Kasa, IOM.

Ana fargabar mutum 63 ne suka mutu, yayin da sauran wadanda suka raya su 38 suka hada da yara ‘yan shekara 12 zuwa 16, kamar yadda mai magana da yawun IOM Safa Msehli ta shaida wa AFP.

‘Yan sandan Cape Verde sun ce an gano kwale-kwalen kamun kifi na katakon ne a ranar Litinin a kan Tekun Atalantika daga nisan kilomita 277 daga gabar tekun tsibirin Sal.

Jirgin ruwan kamun kifi na Sifaniya da ya hango kwale-kwalen ne ya ankarar da hukumomin Cape Verde.

Ma’aikatan agajin gaggawa sun gano gawar mutum bakwai yayin da ake tsammanin sauran mutum 56 sun bata, Msehli ta shaida wa AFP.

“Yawanci idan dai ba a ga mutane ba bayan kifewar jirgin ruwa to kawai ana daukar cewa sun mutu ne,” ta ce.

Yankin Senegal

Kwale-kwalen ya tashi ne daga wani kauyen Senegal da ake kamun kifin mai suna Fasse Boye ranar 10 ga watan Yuli dauke da mutum 101, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen Senegal ta fada a ranar Talata, a yadda ta ji daga bakin wadanda suka rayu.

Dukkan mutanen da ke cikin jirgin ‘yan Senegal ne in ban da mutum daya dan Guinea-Bissau.

Hukumomi a yanzu ba su fadi abin da ya faru da jirgin ba bayan tashinsa. Amma wani jami’i Abdou Karim Sarr, da ke aiki da kungiyar masu kamun kifi ta CLPA ya shaida wa AFP cewa “dukkan wadanda ba a gan su ba sun mutu.”

Tafiya mai hatsari

Hukumomin Cape Verde sun ce sun hada dukkan abubuwan da suka dace don kula da wadanda suka tsira, inda aka kwantar da bakwai daga cikinsu a asibiti bayan isa Sal a ranar Talata.

Ma’aikatar harkokin wajen Senegal ta ce za ta kwashe ‘yan kasarta ba tare da bata lokaci ba. Senegal ta sha fama da irin wadannan bala’o’i a shekarun baya-bayan nan.

Cape Verde tana kan hanyar da dubban ‘yan Afirka ke bi don yin kaura zuwa nahiyar Turai a kokarinsu na guje wa talauci da yaki a kasashensu.

Da yawansu na fatan isa tsibirin Canary na Sifaniya ta bin daya daga cikin hanyoyi mafiya muni, inda suke yawan bin kananan kwale-kwalen da ba sa iya jurar mummunan yanayin tekun.

A watan Janairun bana kawai sai da aka ceto ‘yan ci-rani kusan 90 daga kasashen Senegal da Gambia da Guinea-Bissau da Saliyo a gabar tekun Cape Verde.

AFP