Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya yi kira da a goyi bayan Falasɗinawa, yana mai tir da abin da ya bayyana a matsayin ci gaba da kisan kiyashi da ake yi wa Falasɗinawa a Gaza.
Da yake jawabi ga wani gangamin siyasa da ɗaruruwan matasa suka halarta a babban birnin ƙasar, Daka, Sonko ya zargi manyan ƙasashen duniya da hannu a masifar da aka kwashe wata takwas ana gani ta mutuwa da rusa abubuwa a Gaza.
A kiran da ya yi na kai-tsaye ga Shugaban Senegal Bassirou Diomaye faye, Sonko ya ambato buƙatar Senegal ta goyi bayan ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar da Isra'ila a Kotun Duniya da ke Hukunta Masu Laifukan Yaƙi (ICJ)
"Zan fara bayanina da kiran jama'a su yi addu'ar sa'a guda ga mutane Falasɗinawa da suka yi shahada...mutanen da a yau ake musu kisan kiyashi da haɗin bakin manyan ƙasashe na wannan duniya," a cewarsa.
'Manyan masu hannu a kisan kiyashi'
"Waɗanda suka ayyana kansu a matsayin manyan 'yan dimokraɗiyya, da waɗanda suke kare haƙƙin ɗan adam, su ne a yau manyan masu hannu a kisan kiyashin da ake yi wa Falasɗinawa."
A Disambar bara ne, Afrika ta kudu ta shigar da ƙarar Isra'ila tana zarginta da yi wa Falasɗinawa kisan kiyashi a Gaza.
Fiye da ƙasashe12 ne suka shiga ko kuma suka bayyana aniyarsu ta shiga cikin masu ƙarar Isra'ila kan kisan kiyashi.
Isra'ila ta ci gaba da kai miyagun hare-hare a Gaza tun bayan harin 7 ga watan Oktoba da ƙungiyar Hamas ta kai, duk da ƙudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na tsagaita wuta nan take.