Aljeriya “ta taimaki Faransa wajen kwashe ‘yan kasarta daga Nijar bayan juyin mulki, ta hanyar ba da izinin dakatawa a birnin Algiers,” kamar yadda mai magana da yawun sojin ya bayyana.

Rundunar sojin Faransa a ranar Laraba ta musanta zarge-zargen cewa ta roki izinin Aljeriya don amfani da sararin samaniyarta wajen ayyukan soji a Jamhuriyar Nijar.

Faransa ba ta taba neman wannan izinin ba, don haka babu ma batun kin amincewa daga wajen Aljeriya, in ji wani mai magana da yawun rundunar sojin Faransa kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu.

A ranar Litinin ne gidan rediyon gwamnatin Aljeriya ya sanar da cewa kasar ta ki amincewa da bukatar Faransa ta amfani da sararin samaniyarta wajen kaddamar da duk wasu ayyukan soji a Jamhuriyar Nijar.

Mai magana da yawun rundunar sojin Faransan wanda ya ki a bayyana sunansa, ya kara da cewa Aljeriya ta taimaka wa Faransa wajen kwashe mutanenta daga Nijar, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar wacce ta hada iyaka da Aljaeriya, ranar 26 ga watan Yuli.

Aljeriya “ta taimaki Faransa a wani salo abin kwatance, wajen kwashe ‘yan kasarta daga Nijar ta hanyar ba da izinin dakatawa a birnin Algiers,” kamar yadda mai magana da yawun sojin ya bayyana.

“Dakarun sojin Faransa sun tattauna kamar yadda aka saba da abokan huldarmu na Aljeriya,” in ji mai magana da yawun sojin, yana mai musanta zarge-zargen duk wani tashin hankali da fargaba sakamakon abin da ya faru a Nijar.

Faransa ba ta fito baro-baro ta bayyana aniyarta ta shiga wani aikin soji ba a Nijar, kasar da ta mulka a zamanin mulkin mallaka, inda dakarunta 1,000 zuwa 1,500 ke jibge, amma Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta sha nanata cewa tana goyon bayan duk matsayar da kungiyar ECOWAS ta cimma kan batun.

AA