Kusan mutum 30,000 da ake zargin sun kamu da cutar farankamar biri a bana a Afirka inda akasarinsu sun fito ne daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, in ji Hukumar Lafiya ta Duniya a ranar Litinin.
Fiye da mutum 800 ne suka mutu a fadin nahiyar a bana inda ake zargin cutar ce ta kashe su, in ji hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a cikin rahotonta.
Rahoton ya kara da cewa makwabciyar kasar ta Congo da ke tsakiyar Afirka wato Burundi ita ma ta fuskanci barkewar annobar.
Cutar ta farankamar biri kan bazu idan aka yi mu'amula, inda a wani lokacin ba ta nuna alamu, a wani lokacin kuma tana da hatsari.
Cutar kan nuna alamun mura hakan kuma marurai kan feso a jiki.
WHO ɗin ba ta bayar da alƙaluman da za a kwatanta da shekarun baya ba.
Sashen lafiya na Ƙungiyar Tarayyar Afirka ya ce an samu mutum 14,957 da suka kamu da cutar da kuma mutum 739 da cutar ta kashe daga ƙasashe bakwai na nahiyar a 2023 - wanda hakan ke nuni da ƙaruwar masu kamuwa da cutar idan aka kwatanta da shekarar 2022.
Tallafin kuɗi domin yaƙi da cutar
An samu mutum 29,342 da ake zargin sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutum 812 a fadin Afirka daga watan Janairu zuwa 15 ga watan Satumba na wannan shekara, a cewar rahoton na WHO.
Jumullar mutum 2,082 da aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin duniya a cikin watan Agusta kadai, mafi girma tun watan Nuwamban 2022, in ji WHO.
A ranar Asabar, asusun bankin duniya na annobar cutar ya ce zai bai wa kasashen Afirka goma dala miliyan 128.89 don taimakawa wajen yakar annobar.