Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon jiya, kamar yadda alkaluman da hukumar zaben kasar ta fitar ranar Asabar suka nuna.
Wannan ne karo na biyu da shugaban kasar ke lashe zaben, wanda masu sanya ido na kasashen duniya suka ce bai kai mizanin sahihin zabe na dimokuradiyya ba.
Mnangagwa, mai shekara 80, ya lashe kashi 52.6 na kuri'un da aka kada yayin da babban mai hamayya da shi, Nelson Chamisa, mai shekara 45, ya samu kashi 44, a cewar hukumar ta Zimbabwe Electoral Commission (ZEC).
"An ayyana Mnangagwa Emmerson Dambudzo na jam'iyyar ZANU-PF a matsayin sahihin mutumin da aka zaba a shugaban kasar Zimbabwe," a cewar shugabar hukumar zaben, Mai Shari'a Chigumba a taron manema labarai.
'Yan kasar Zimbabwe sun kada kuri'unsu ranar Laraba da Alhamis ko da yake an yi ta samun tsaiko abin da 'yan hamayya suka yi zargin cewa "magudi" da "takura masu zabe" ne.
Ranar Juma'a masu sanya ido na kasashen duniya sun ce zaben na Zimbabwe bai cika sharudan kasashen duniya ba.
Kasashen kudancin Afirka sun sanya ido sosai kan zaben a matsayin wani zakaran-gwajin-dafi kan farin-jinin jam'iyyar ZANU-PF ta su Mnangagwa, wadda shekaru 43 da ta yi tana mulki suka jefa 'yan kasar cikin tabarbarewar tattalin arziki da mulkin kama-karya.
Chigumba ta ce Mnangagwa ya samu kuri'u fiye da miliyan 2.3, yayin da Chamisa ya samu sama da kuri'a miliyan 1.9.
Ba za a je zagaye na biyu na zaben ba, tun da dai shugabana kasar ya samu fiye da rabin kuri'un da aka kada. Alkaluma sun ce masu kada kuri'a sun kai kashi 69 cikin dari na mutanen da suka yi rajistar zabe.
Mr Mnangagwa, wanda ake yi wa lakabi da "Kada" saboda rashin tsoronsa, ya hau mulki ne bayan wani juyin mulki da aka yi wa dadadden shugaban kasar Robert Mugabe a 2017.
Shekara daya bayan haka, ya sha da kyar a hannun Chamisa a zaben shugaban kasar wanda 'yan hamayya suka bayyana a matsayin mai cike da magudi.