Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da Majalisar Dokokin Jihar a gaban kotu dangane da zargin da 'yan majalisar suke yi masa na karkatar da naira biliyan 432 da kuma barin jihar da ɗimbin bashi.
El-Rufai ya shigar da ƙarar ne a gaban Kotun Tarayya ta Kaduna domin a bi masa haƙƙinsa.
Abdulhakeem Mustapha wanda shi ne lauyan na El-Rufai ya ƙalubalanci wani rahoto da majalisar ta gabatar na zargin tsohon gwamnan da wasu muƙarrabansa da aikata almundahana.
A ƙarar da tsohon gwamnan ya shigar, ya buƙaci kotun ta ayyana rahoton da majalisar dokokin ta gabatar a matsayin mara inganci inda yake zargin ba a ba shi damar sauraron ɓangarensa ba kafin yi masa wannan zargin.
Baya ga Majalisar Dokokin Kaduna, Kwamishinan Shari’a kuma Antoni Janar na Jihar na daga cikin waɗanda El-Rufain ke ƙara.
A farkon watan nan ne na Yuni Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta buƙaci hukumomin da ke yaƙi da rashawa su binciki tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai da wasu muƙarraban gwamnatinsa kan zargin cin amanar aiki da halasta kuɗin haram
Wannan na zuwa ne bayan bincike na musamman da wani kwamitin majalisar ya gudanar ƙarƙashin jagorancin Henry Zacharia.
A cewar rahoton da Zacharia ya gabatar, yawancin bashin kuɗin da aka samu a karkashin gwamnatin El-Rufai, ba a yi amfani da su yadda suka dace, kuma a wasu lokuta, ba a bi ka’idojin da suka dace wajen samun bashin ba.
Don haka kwamitin ya bayar da shawara ga hukumomin yaƙi da rashawa su gudanar da bincike da gurfanar da tsohon gwamnan da wasu jami’an gwamnatin kan zargin amfani da mukami domin bayar da kwangiloli ba tare da bin ƙa’ida ba, da karkatar da kuɗaɗen jama’a, da kuma kuɗaɗe.