Ƙungiyar Raya Tattalin Arziki ta Ƙasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta yi Allah-wadai da harin ta’addancin da aka kai wata cibiyar sojoji a birnin Bamako na Mali ranar Talata.
“ECOWAS ta kuma aike da ta’aziyyarta ga gwamnati da al’ummar Jamhuriyar Mali da kuma iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su,” kamar yadda wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Laraba a Abuja ta bayyana.
Sanarwar ta ce ƙungiyar na ƙara yin Allah-wadai da dukkan hare-haren ta’addanci da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya na jama’ar Yammacin Afirka.
ECOWAS ta kuma jaddada matsayarta ta goyon bayan duk wani shiri da zai tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a yankin.
A ranar Talata ne aka wayi gari wasu mahara ɗauke da makamai suka kai hari wata cibiyar horas da Jandarmomi a Bamako babban birnin kasar Mali, amma daga baya an shawo kan lamarin, in ji sojojin ƙasar.
Rundunar Sojojin Mali ta ce wasu ‘yan ta’adda sun yi yunƙurin kutsawa cikin makarantar Faladie Gendarmerie da ke Bamako babban birnin kasar.