Ƙungiyar ECOWAS ta cire takunkumin da ta saka wa Jamhuriyar Nijar wanda ya haɗa da batun rufe iyaka da kuma kasuwanci.
Ta bayyana haka ne a ranar Asabar a yayin taron da ta gudanar a Abuja, babban birnin Nijeriya. Haka kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa ƙasashen Mali da Guinea.
''Za a janye waɗannan takunkumai nan-take," in ji shugaban majalisar ECOWAS Omar Alieu Touray bayan taron ƙungiyar.
Za a janye takunkuman da aka saka wa Nijar ne "bisa dalilai na jinƙai” domin sauƙaƙa wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke sha, a cewar Touray a hira da manema labarai. Ya ƙara da cewa: “Amma akwai takunkuman da aka sanya wa ɗaiɗaikun jama'a da kuma na siyasa waɗanda za su ci gaba da aiki."
Tun a farkon watan nan ne Mali da Burkina Faso da Nijar suka sanar da ficewarsu daga ƙungiyar kan niyyarsu ta barin ƙungiyar, lamarin da ya ta'azzara rikicin da suke yi da ita.
Sai dai tun a jawabinsa na farkon Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa: "Dole ne mu sake nazari kan hanyar da muka ɗauka ta neman tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashe mambobinsu.”
“Saboda haka ina kira a gare su da su sake nazari dangane da matakinsu na ficewa daga gidansu haka kuma kada su ɗauki ƙungiyarmu a matsayin abokiyar gaba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
An shafe lokaci mai tsawo ana dambarwa tsakanin ECOWAS da Nijar da Burkina Faso da Mali, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
A ranar Laraba ne tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya kuma ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS, Janar Yakubu Gowon ya yi kira a cire takunkuman da aka sanya wa ƙasashen da sojoji suka yi juyin mulki a Yammacin Afirka.
A wani taro da ECOWAS ta gudanar a Abuja, Janar Gowon ya yi kira ga shugabannin mulkin sojin Burkina Faso, Mali da Nijar su janye aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar.
Ya roƙe su cewa "Don girman Allah ku dawo."