Shugaban ECOWAS Bola Tinubu  ya ce kungiyar za ta yi amfani da “karfi” a yunkurin kubutar da Shugaba Mohamed Bazoum./Hoto: AFP

Shugabannin Kungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afirka ECOWAS sun bai wa sojojin Nijar wa'adin mako daya su mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.

Sun ba da umarnin ne a taron da suka gudanar ranar Lahadi a Abuja babban birnin Nijeriya.

Shugabannin na ECOWAS sun ce za su yi amfani da karfin soji kan sojojin idan ba su bi umarninsu ba.

Kungiyar ta yanke shawarar sanya takunkumi na harkokin kudi da tafiye-tafiye kan sojojin.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wani jami'in ECOWAS yana cewa za a sanya takunkumin ne nan take.

Wasu daga cikin matakan da aka dauka kan sojojin sun hada da rufe iyakokin kasashen ECOWAS da ke makwabtaka da Nijar da kuma sanya takunkumin hana tafiye-tafiye kan sojojin.

Shugaban ECOWAS Bola Tinubu, wanda shi ne shugaban Nijeriya, ya ce kungiyar za ta ci gaba da kallon Bazoum a matsayin shugaban Nijar.

“Afirka ta girma. Mun yi watsi da juyin mulki da yin kutse a tsarin mulki,” in ji Tinubu a jawabin da ya yi a wurin taron.

‘Dole mu dauki tsattsauran mataki’

“Sojoji suna tsare da daya daga cikinmu, wato Bazoum. Hakan cin-fuska ne a gare mu baki daya kuma dole mu dauki tsattsauran mataki. Da farko, mu kare rayuwar Shugaba Bazoum. Yin katsalandan cikin harkokin dimokuradiyya ya jefa al'ummar Nijar cikin yanayi na rashin tabbas,” in ji Shugaba Tinubu.

“Na yi wa wasu daga cikinku bayani game da matakan da muka dauka domin yin raddi kan wannan kutse da kuma tabbatar da cewa dan uwanmu Shugaba Bazoum yana cikin koshin lafiya sannan a maido da tsarin dimokuradiyya a Nijar," a cewar Shugaba Tinubu.

Lalubo bakin zaren

A gefe guda, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Déby Itno ya isa Jamhuriyar Nijar ranar Lahadi inda ya gana da sojojin kasar don lalubo bakin zaren game da matsalar da ta fada a ciki sakamakon juyin mulkin makon jiya.

Deby  da kansa ne ya ga ya kamata a shiga tsakani domin ganin an warware matsalar Jamhuriyar Nijar, a cewar kakakin gwamnatin Chadi./Hoto: TRT Afirka

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato kakakin gwamnatin Chadi Aziz Mahamat Saleh yana cewa Janar Déby ya je Yamai ne domin "ganin matakin da zai iya dauka don shawo kan wannan matsala."

Ya kara da cewa shugaban da kansa ne ya ga ya kamata ya shiga tsakani domin ganin an warware matsalar Jamhuriyar Nijar wadda ke makwabtaka da kasarsa.

TRT Afrika