Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS ta yi kira ga Turkiyya ta ƙara tallafi ga ƙasashen da ke yankin a ƙoƙarin su na daƙile matsaloli n atsaro.
Shugaban hukumar ƙungiyar ta ECOWAS , Omar Touray, ya yi wannan kiran ne a lokacin da jakadan Turkiyya a Nijeriya mai barin gado, Hidayet Bayraktar, ya kai masa ziyarar bankwana ranar Talata, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya ruwaito.
Touray ya yaba wa rawan da Turkiyya ke takawa a Afirka da kuma duniya , yana mai kira gareta da ta ci gaba da taiamakawa wajen yaƙi da ƙungiyoyin 'yan ta'dda da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Yammacin Afirka.
"Turkiyya babbar ƙawar hulɗa ce a Afirka kuma ƙawar hulɗa mai gata ce ga ECOWAS. Ana yaba wa shugabancin ta tare da gamsuwa da ita a faɗin nahiyar Afirka," in ji Touray.
"Ƙalubalen da ECOWAS ta fi fama da shi ne rashin tsaro, kuma babu ɗaya daga cikin mabobinta da za ta iya fuskantar sa ita kaɗai ," a cewarsa.
A nasa ɓangaren, jakadan Turkiyya mai barin gado, Hidayet Bayraktar, ya nanata jajircewar Turkiyya wajen zurfafa tallafinta magance matsalolin masu tsattsauran ra'ayi da kuma ta'addanci tare da inganta zaman lafiya da tsaro a yankin.
Turkiyya da ƙasashen Afirka sun ƙarfafa hulɗarsu ta soji da tattalin arziƙi da kuma al'adu yayin da Ankara take sake zama zaɓi a maimakon ƙasashen yamma masu ƙarfin tattalin arziƙi.
Wasu ƙasashen Afirka sun sayi kayayyakin soji ciki har da jirage mara matuƙa daga Turkiyya domin inganta ƙarfin sojinsu.